Manoma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Manoma
sana'a
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na agricultural worker (en) Fassara da field crop and vegetable growers (en) Fassara
Field of this occupation (en) Fassara noma da farming (en) Fassara
ISCO-88 occupation class (en) Fassara 6111 da 9212
manoman masara
manomi janye da shanun huda

Manoma jam'in kalma ce ta manomi sannan kalmar ta samo asali ne daga Noma. Manoma: suke noma dukkan kayan masarufi na abinci kamar irinsu hatsi, borkono, tarugu, tumatur, tattasai, alaiyahu, kabeji, latas da dai sauran su. Manoma sun kasu zuwa kashi biyu ne (2). Akwai masu noman rani akwai kuma masu na Damina da kuma na zamani duk da kuma dai yanzu kusan duka manoma suna amfani da kayayyakin zamani. Sai dai wani lokacin manoma suna fuskantar kalubale da matsalolin rashin kayan aiki da don saboda rashin tallafin daga gwamnati zaka hasashe ya nuna kaso kusan saba'in (70) cikin ƴan Najeriya manoma ne amma saboda babu cikakkun kayan aiki da tallafi shi yasa harkokin noma ba su bunƙasa ba.[1]

manomi yana huɗa da galmar shanu a cikin gona

Nau'in manoma[gyara sashe | gyara masomin]

1- Manoman Kasuwanci.

2- Manoman Infaki.

Su kuma manoman kasuwaci suna nomane sabida su sayar wa yan kasuwa bayan sun girbe abinda suka noma imma dai hatsi ko makamancin haka domin su samar wa kansu da iyalansu kudin shiga don more rayuwa. yawancin yan wa innan bangaren mutanen birni ne, amman suna amfani ne da kudinsu su biya mutanen kauye sai suyi musu aikin noman kodai lokacin rani ko na damuna.

Manoman Infaki, duk ita kalmar Infaki kalmar larabci da ta ginu daga 'Anfaka, Yunfiku, Infaakan'

wace take nufin abun da aka kashe na kudi ko aka ciyar, manoman Infaki su suna yin noma ne saboda ciyar da iyalansu kawai. Sannan kuma suna yin noma ne kan gwargwadon abunda iyalansu zasu ci kuma su taimaki wasu,

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.bbc.com/hausa/news/story/2010/03/100302_foodseries_farmers