Jump to content

All Progressives Congress

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
All Progressives Congress
Bayanai
Gajeren suna APC
Iri jam'iyyar siyasa
Ƙasa Najeriya
Ideology (en) Fassara Dimokuradiyya zamantakewa, Tsarin zamantakewar Afirka, federalism (en) Fassara, populism (en) Fassara, social conservatism (en) Fassara da progressivism (en) Fassara
Political alignment (en) Fassara Bangaren hagu
Mulki
Shugaba Adams Aliyu Oshiomhole
Hedkwata Abuja
Tarihi
Ƙirƙira 2013
Founded in Abuja
Mabiyi Congress for Progressive Change (en) Fassara, All Nigeria Peoples Party, Action Congress of Nigeria da All Progressives Grand Alliance

allprogressivescongress.org

Shugaba buhari shene shugaban farko a jam'eyan A.P.C
All Progressives Congress
shugaba Bola Ahmed Tinubu Shugabar Na biyu a Jam'ir APC

Jam'iyyar APC jam'iyyar siyasa ce mai mulki a Najeriya, wadda aka kafata a ranar 6 ga watan Fabrairu na shekarar 2013, gabannin zuwan zaɓen shekarar 2015.[1] [2] [3] Ɗan takarar APC a matakin shugaban kasa shine Muhammadu Buhari ya kuma lashe zaɓen shugaban ƙasar da kusan kuri'u miliyan 2.6. [4] Shugaban ƙkasa Goodluck Jonathan yayi nasara a ranar 31 ga watan Maris. [5] Wannan shi ne karo na farko a tarihin siyasa cewa jam'iyyun siyasa na adawa sun kayar da wata jam'iyya mai mulki a babban zaɓe, kuma ɗaya daga cikin wutar lantarki ta sauya zaman lafiya daga wata jam'iyyar siyasa zuwa wata. [6] Bugu da kari, APC ta lashe rinjaye mafi yawa a majalisar dattijai da majalisar wakilai a zaben shekarar 2015, sannan kuma sun ansa mulkin kasar a hannun jam'iyya mai mulki.

[7][8]Me ya bambanta haɗakar APC da ta ADC?

A ranar Laraba wasu gaggan ƴan hamayya a Najeriya suka sanar da dunƙulewarsu a jam'iyyar ADC domin yin haɗaka a ƙalubalanci ƙudirin shugaba Bola Tinubu na tazarce a 2027.

Ƴan siyasar, ƙarƙashin jagorancin sanata David Mark, sun haɗa da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi da Rotimi Amaechi da Rauf Argebesola da Malam Nasiru El- Rufai da dai sauran jiga-jigan ƴan siyasa daga kudu da arewacin ƙasar. Irin wannan haɗaka ce dai a shekarar 2015 ta bai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari damar jagorancin ƙasar, sakamakon ƙalubalantar shugaban lokacin mai neman tazarce, Goodluck Ebele Jonathan a ƙrƙashin jam'iyyar APC. Hakan ne ya sa ƴan Najeriya ke tambayar ko akwai bambanci tsakanin jam'iyyun haɗakar guda biyu?

Sabon salon haɗaka

[gyara sashe | gyara masomin]

Malam Kabiru Sufi masanin siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a kano wato CAS ya ce saɓanin haɗakar da aka cimma kafin kafa jam'iyyar APC, inda aka rusa wasu jam'iyyu sannan wasu suka bar jam'iyyunsu kafin aka gina haɗakar, haɗakar ADC ta sha bamban.

"A wannan karon ƴan jam'iyyun ne suka fito daga jam'iyyunsu suka shiga jam'iyyar da take da rijista. Wani salo ma da ya fito a karon farko a siyasance shi ne waɗanda suka shiga jam'iyyar sun tarar da jagoranci a jam'iyyar ADC amma kuma jjagororin suka amince su sauka a yi sabon fasali domin damawa da kowane ɓangare.

Saɓanin a haɗakar da aka yi da ta haifar da jam'iyyar APC, inda ƴan siyasar suka narkar da jam'iyyunsu suka kafa wata sabuwar jam'iyya." In ji Malam Kabiru Sufi.

Malam Kabiru Sufi ya ƙara da cewa wani banbancin da ke tsakanin haɗakar guda biyu shi ne yadda wasu jam'iyyu ke yin barazana ga ƴaƴansu da har yanzu ba su ayyana fitarsu daga jam'yyun ba amma kuma ana ganin su a tarukan hadaƙar ta ADC.

An Kafa jam'iyyar ce a cikin watan Fabrairun shekara ta 2013, a sakamakon wani ƙawance na jam'iyyun siyasan Najeriya guda uku mafi girma daga cikin jam'iyyun adawa - da Action Congress of Nigeria (ACN), da Congress for Progressive Change (CPC), da All Nigeria Peoples Party (ANPP) - da kuma wata Kungiya na Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), ta hada hannu ne a kan Jam'iyyar Jama'a.[9][10] Sakamakon yarjejeniya ta Tom Ikimi , wanda ya wakilci ACN; Sanata Annie Okonkwo a madadin APGA; Ibrahim Shekarau , shugaban kwamitin tarayyar ANPP; da kuma Garba Shehu, shugaban kwamitin Jam'iyyar CPC.[11][11] Abin takaici, kasa da shekaru 2 kafin nasarar lashe zaben a zaben shekara ta 2015 . Annie Okonkwo , Tom Ikimi da Ibrahim Shekarau sun yi murabus daga jam'iyyar kuma sun shiga jam'iyar PDP.

Shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa
Shugaba mataimakin shugaba Za ~ e Sakamakon
Muhammadu Buhari Yemi Osinbajo 2015-2019 Won

.

  1. "The Merger This Time!". PM News. 13 February 2013. Retrieved 15 February 2013.
  2. Maram, Mazen (7 February 2013). "Nigerian Biggest Opposition Parties Agree to Merge". Bloomberg. Retrieved 11 February 2013.
  3. Opoola, Murtala (10 February shekarar 2013). "Nigeria: Welcome, All Progressives Congress". AllAfrica. Retrieved 11 February 2013. Check date values in: |date= (help)
  4. Empty citation (help)
  5. Empty citation (help)
  6. "Nigeria makes history in presidential election". 31 March 2015. Retrieved 31 March 2015.
  7. ^ "APC wins 214 House of Reps' seats" . Punch . 8 April 2015. Archived from the original on 21 April 2015. Retrieved 8 April 2015.
  8. ^ "APC wins 64 seats in Senate" . Punch . 1 April 2015. Archived from the original on 1 April 2015. Retrieved 1 April 2015
  9. ^ "Update: ACN, ANPP, APGA, CPC merge into new party, APC - Premium Times Nigeria" . 7 February 2013. Retrieved 22 January 2020.
  10. ^ Akor, Ambrose (18 April 2013). "Nigeria's Key Opposition Party Approves Merger Plan" . Bloomberg . Retrieved 6 May 2013.
  11. 1 2 ^ and Basirat Nahibi Agbakwuru, Johnbosco (10 February 2013). "Nigeria: New Party – Buhari, Tinubu, Threaten Jonathan With Armoured Personnel Carrier, APC" . AllAfrica . Retrieved 12 February 2013.

Hanyoyin waje

[gyara sashe | gyara masomin]