Jump to content

Usman Saidu Nasamu Dakingari

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Usman Saidu Nasamu Dakingari
Gwamnan Jihar Kebbi

29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015
Adamu Aliero - Aminu Musa Habib Jega (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 13 Satumba 1959 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Usman Sa'idu Nasamu Dakingari (an haife shi ranar 13 ga watan Satumban, 1959). ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya yi gwamnan jihar Kebbi daga shekarar 2007 zuwa 2015. An zaɓe shi gwamna a watan Afrilun 2007, inda ya hau mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2007. Dan jam'iyyar PDP ne.[1] An sake zaɓen shi a ranar 26 ga watan Afrilun shekarar 2011.[2]

Sai dai a ranar 24 ga watan Fabrairun 2012. kotun koli ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kebbi ta yanke na soke zaɓensa, sannan ta ba da umarnin sake gudanar da zaɓe cikin kwanaki 90. Harwayau an sake zaɓen shi a ranar 31 ga watan Maris ɗin shekarar 2012. kuma ya hau mulki a ranar 2 ga watan Afrilu.[3]

Kuruciya da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi shi a Jihar Kebbi, ranar 13 ga watan Satumban 1959 a Dakin Gari.

Ya halarci Kwalejin (Arts & Science) ta Jihar Sakkwato (1979 – 1981), da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (1980 – 1984), inda ya yi digirin farko a fannin Nazarin Kasa (Geography).

Yayi hidimar ƙasa a jihar Ondo, sannan yayi aiki a matsayin jami'in tsare-tsare a ma'aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Sokoto (1985-1989).

A shekara ta 1989, ya shiga hukumar kwastam ta Najeriya a matsayin mai kula da kwastam.

Gwamnan jihar Kebbi

[gyara sashe | gyara masomin]
Jihar Kebbi a Najeriya

Dakingari bayan ya bar aikin kwastam ya yi nasarar tsayawa takarar gwamnan jihar Kebbi a watan Afrilun 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

An sake zaɓen Dakingari a ranar 26 ga watan Afrilun shekarata 2011.[2] A ranar 18 ga watan Mayun shekarar 2011 abokin hamayyarsa na jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC), Malam Abubakar Abubakar, ya kalubalanci zaɓen bisa dalilan rashin bin ka’ida.[4] Daga bisani kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kebbi ta soke zaɓen tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe. Wata kotun ɗaukaka ƙara da ke Sokoto ta soke soke hukuncin a ranar 29 ga watan Disamba, shekarar 2011, to amma ba ta bayar da dalilin yanke hukuncin ba sai ranar 23 ga watan Janairun shekarar 2012, fiye da kwanaki 60 da sauraron karar. A ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2012 ne kotun kolin Najeriya ta yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke saboda jinkirin da aka samu, ta bayyana soke zaben tare da ba da umarnin sake gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 90. Aminu Musa Habib Jega, kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi, ya zama mukaddashin gwamna a madadinsa.[5]

Yana da ya'ya mata uku: Asmau, Zubaidah da Zainab - diyar Marigayi Shugaba Umaru 'Yar'aduwa.[6] Sun haifi 'ya'ya uku tare da Maryam babba, Musa da Umar.[7]

Duba sauran wasu abubuwan

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Jerin Gwamnonin Jihar Kebbi
  1. "Governor Sa'idu Usman Nasamu Dakin Gari of Kebbi State". Nigeria Governors' Forum. Retrieved 2010-01-01.
  2. 2.0 2.1 Sulaimon Olanrewaju & Olayinka Olukoya (28 April 2011). "GOV ELECTION: The winners are Ajimobi, Fashola, Amaechi, Amosun, Abdulfatah, Akpabio, Aliyu, Dakingari, Orji, Chime, Kwankwaso..." Nigerian Tribune. Archived from the original on 30 April 2011. Retrieved 28 April 2011.
  3. GARBA MUHAMMAD; ELIZABETH ARCHIBONG & HENRY OMUNU (2 April 2012). "Nigeria: Dakingari Wins Kebbi Amid Controversy". The Moment (London). Retrieved 2012-04-05.
  4. IHUOMA CHIEDOZIE (February 25, 2012). "S'Court sacks Kebbi gov, Dakingari". The Punch. Archived from the original on March 6, 2012. Retrieved March 5, 2012.
  5. Solomon Chung; Atika Balal; John Chuks Azu, Abuja & Umar Jibrilu Gwandu (25 February 2012). "Supreme Court sacks Kebbi governor". Weekly Trust. Archived from the original on 2012-02-28. Retrieved 2012-03-05.
  6. Kabir, Hajara Muhammad (2010). Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
  7. Saka Ibrahim (27 July 2007). "Yar'Adua's daughter now Kebbi's First Lady". This Day (Lagos). Retrieved 2010-01-18. [dead link]