Barack Obama

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Barack Obama
Barack Obama
shugaban Amurika na 44
Lokacin da yazama shugaba 20 Jauwari 2009
ya karbi ragamar mulki daga George W. Bush
mataimakin sa Joe Biden
ya bayar da mulki ga Donald Trump
gurin zama Honolulu, Hawaii
matarsa Michelle Obama
jam'iyyr Democrats

An aifi Barack Hussain Obama ranar 4 ga watan Oguster na shekara ta 1961 a birnin Honolulu dake yankin Hawai a ƙasar Amurika. Tun yana ɗan shekaru biyu da aihuwa iyayensa suka rabu, ya cigaba da zama tare da ma´haifiyarsa. Mahaifinsa musulmi ne dan kasar Kenya a nahiyar Afirka, ya bar Amurika bayan ya bar matarsa a Amurka inda ya koma gida Kenya. ya kuma zama minista a cikin gwamnatin shugaban ƙasa na farko, wato Jomo Keniyatta, kamin Allah ya amshi ransa, a shekara ta 1982 a cikin haɗarin mota.

A lokacin da ya samu shekaru shida, har zuwa shekaru 10, Barack Obama ya bi ma´haifiyarsa zuwa ƙasar Indonesia inda suka yi zama na shekaru huɗu. Sai a shekara ta 1971 ya komo Honolulu, inda ya ci gaba da karatu. Yayi karatu a jami´ar Kaliforniya da kuma ta Kolumbiya a birnin New York. Bayan ya kamalla karatu, a jami´a, Obama ya fara aiki a matsayin jami´i, ta fannin lissafin kudi. To saidai bai jima ba yana wannan aiki ya kuma koma ƙarin ilimi, inda a shekara ta 1991 ya fito da digrin digirgir ta fannin sharia´a. Barack ya jima ya na kwaɗayin shiga siyasa, amma sai a shekara ta 1996 haƙƙarsa ta cimma ruwa, inda karon farko a ka zaɓe shi a matsayin dan majalisa a mazaɓarsa ta yankin Ilinois.

A tsawan watani 18 Barack Obama na fafatawa da matar tsofan shugaban ƙasar Amurka, wato Hilary Klinton domin samun tabaraki daga jam´iyar Demokrate don tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasar Amurikar.

Kafin zabe[gyara sashe | Gyara masomin]

A shekara ta 2004 ya tsaya takara a Majalisar Dokoki A wani matakin da wasu ke dangatawa da "rabbo rabbabe", ba zato ba tsammani, Barack Obama ya kai gaci, ya kayar da abokiyar hamayar tasa. A duk tsawan wannan lokaci Obama ya bayyana kansa a matsayin gwarzo, duk da cewar da dama na masa zargin rashin ƙwarewa cikin harkokin siyasa, idan aka kwatanta shi da Hilary Klinton, ko kuma da ɗan takara jam´iyar Republicain John Makain, mai shekaru 72 a duniya,wanda kuma ya laƙanci ƙabli da ba´adin siyasa, a ciki da wajen Amurika. Ta fannin rubuce rubuce,Barack Obama, ya rubuta littatafai guda biyu, inda a ɗaya daga cikin su, yayi tarihin rayuwar baƙaƙe a Amurika, tare da bayyana yadda a matsayinsa na baƙin ba´amurike ya gudanar da yarintarsa. Barack Obama,na da aure da kuma ´yaya,´yan mata guda biyu.

kafin ya tsaya takara, da shi Sanata ne a Jam'iyar dimukaratic ta Jihara Illinois acikin wannan lokacin a 4 ga 2005 zuwa 16 ga shekara ta 2008 kuma shene dan afirka na farko a majalisar wakilai Amurika kuma shine dan asalin Afirka na farko da yatsaya takarar shugaban Amurika a Jam'iyar dimucraic sannan ya kayar da abokiyar takatarsa Hillary Clinton.