Jump to content

White House

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
White House
White House
White House Complex
Fayil:White-house-floor1-red-room.jpg, White-house-floor1-green-room.jpg
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaTarayyar Amurka
Federal district (en) FassaraDistrict of Columbia (en) Fassara
City in the United States (en) FassaraWashington, D.C.
Coordinates 38°53′52″N 77°02′12″W / 38.8978°N 77.0367°W / 38.8978; -77.0367
Map
History and use
Reconstruction1949 - 1952

Burning of Washington 1814
Ƙaddamarwa1 Nuwamba, 1800
Mai-iko Federal Government of the United States (en) Fassara
Manager (en) Fassara National Park Service National Park Service
Amfani Fadar Gwamnati
Occupant (en) Fassara shugaban Tarayyar Amurka
first family of the United States (en) Fassara
Karatun Gine-gine
Zanen gini James Hoban (en) Fassara
Launi ██ Fari
Style (en) Fassara Neoclassical architecture (en) Fassara
Tsawo 21.33 m
Floors 4
Faɗi 46.3 meters
Tsawo 51.2 meters
Facilities elevator
Heritage
NRHP 19600001
Visitors per year (en) Fassara 826,300
Contact
Address 1600 Pennsylvania Avenue NW, Washington, DC 20500
Waya tel:+1-202-456-1414 da tel:+1-202-456-1111
Offical website
Aerial view of the White House complex, from north. In the foreground is Pennsylvania Avenue, closed to traffic. Center: Executive Residence (1792–1800) with North Portico (1829) facing; left: East Wing (1942); right: West Wing (1901), with the Oval Office (1909) at its southeast corner

White House, Farin Gida itace gidan Gwamnati kuma wurin aikin Shugaban kasar Tarayyar Amurka. Tana nan ne a 1600 Pennsylvania Avenue Arewa maso yamma a birnin Washington, D.C. kuma takasance itace gidan kowane shugaban Tarayyar Amurka tun daga kan John Adams a 1800. Kalmar "White House" ana amfani dashi amatsayin metonym ga shugaban kasa da mukarraban gwamnatin sa.

Wanda ya tsara ginin White House shine Mai zane-zanen gidaje haifaffen kasar Ireland wato James Hoban[1] acikin tsarin neoclassical. Hoban modelled the building on Leinster House a Dublin, ginin da ayau yake dauke da Oireachtas, majalisar kasar Ireland. An gina shi a tsakanin 1792 da 1800 tare da amfani da Aquia Creek sandstone akai masa fenti da fari. Sanda Thomas Jefferson yakoma gidan a 1801, Ya (tare da mai zane-zane Benjamin Henry Latrobe) sun kara colonnade daga kowane bangare, wanda ya lullube stables da storage.[2] A 1814, lokacin Yakin 1812, Sojin Birtaniya sun banka wa gidan wuta a wani abunda suka kira Kona Washington, wanda ya lalata ciki da kone yawan cin wajen gidan. Sai aka sake sabunta gina ta cikin wuri, sannan shugaban James Monroe yakoma bangaren da aka gyara Gidan Zartaswan a October 1817. Ginin waje yacigaba da gudana tareda karin semi-circular South portico a 1824 da kuma North portico a 1829.

Sabada cinkoson mutane acikin gidan zartaswan, shugaba Theodore Roosevelt yasa aka mayar da dukkanin ofisoshin aiki komawa sabon ginin West Wing a 1901. Shekaru takwas bayan nan a 1909, Shugaba William Howard Taft yakara fadada West Wing kuma ya kirkiri Oval Office, wanda aka komar dashi bayan fadada bangaren. Acikin babban gidan, hawa na ukun gidan attic an mayar dashi yakoma gidajen zama a 1927 ta hanyar kara rufin hip na gidan da dogayen shed dormers. Sabon ginin East Wing anyi amfani dashi amatsayin wurin reception na bukukuwan alumma; Colonnades na Jefferson ita ta hada sabbin wings din da aka gina. An kammala canja East Wing a 1946, da samar da karin filin ofishi. A 1948, bangon ginin wajen gidan da bimi na katako dake ta ciki anga sun kusa fadi. Karkashin Harry S. Truman, an canja fasalin dakunan cikin gidan dukkanin su da gina sabbin new internal load-bearing steel frame a jikin bangonsu. Da aka kammala sai aka sake ginin dakunan ciki.

White House na yanzu na dauke da fadar gwamnati, West Wing, East Wing, da Eisenhower Executive Office Building—da tsohon State Department, wanda ayanzu ya kunshi ofisoshin ma'aikatan shugaban kasa da na mataimakinsa, da Blair House, masaukin baki. Fadar gwamnati gini ne mai hawa shida, wanda Ginin kasa, State Floor, Second Floor, da Third Floor da kuma two-story basement. Ginin tarihi ne na Tarayyar Amurka wanda National Park Service ke da hakkin mallaka kuma tana daga cikin bangare na President's Park. A 2007, an sanya ta na biyu[3] a cikin jeri na American Institute of Architects "America's Favorite Architecture".

Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Inside the White House: History". WhiteHouse.gov. Retrieved January 21, 2017.
  2. Michael W. Fazio and Patrick A. Snadon (2006). The Domestic Architecture of Benjamin Henry Latrobe. The Johns Hopkins University Press. pp. 364–366.
  3. to the Empire State Building