Azare

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Garin Azare dai gari ne mai tarihi a kasar hausa yana da sarkin yanka sunan sarkin kuwa shine Alh Dr Muhammed Kabir Umar CON. ana ce masa Sarkin katagum Sunan karamar hukumar katagum ne sannan karamar hukumar ta gabas tayi iyaka da damban ta yamma kuma tayi iyaka da shira da jama'are ta kudu kuma tayi iyaka da misau ta arewa kuma tayi iyaka da itas gadau garin azare yana cikin arewacin bauci kuma shine gari na biyu mafi girma bayan garin bauchi kuma garin na azare yana da gidajen talabijin guda biyu akwai NTA channel 6 akwai BATV channel 44 kuma yana da gidan rediyo guda daya wadda ake ce dashi BRC FM kan mita 94.6 yana da anguwanni da dama amma manyan ciki sune akwai matsango daga kudanci sannan akwai nasarawa daga tsakiya sannan akwai tsakuwa daga gabaci sannan akwai kasuwar kaji daga yammaci sannan akwai anguwar dan kawu daga arewaci sannan akwai kauyuka da suke zagaye dashi daga gabas akwai dalli daga yamma akwai bulkacuwa daga kudu akwai da isawa da zabi daga arewa kuma akwai duhuwar kura da gadau Goo