Shehu Idris

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Shehu Idris
Masarautar Zazzau 01.jpg
18. Sarkin Zazzau

8 ga Faburairu, 1975 - 20 Satumba 2020
Muhammadu Aminu (en) Fassara - Ahmed Nuhu Bamalli
Rayuwa
Haihuwa Zariya, 20 ga Faburairu, 1936
ƙasa Najeriya
Mutuwa Kaduna, 20 Satumba 2020
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mai koyarwa
Imani
Addini Musulunci

Shehu Idris An haife shi a shekarar 1936 ya rasu a shekara ta 2020, ya kasance shine Sarkin Zazzau na goma sha takwas 18 a jerin sarakunan wadanda su kai mulkin zazzau ko Zaria dake Jihar Kaduna, a sarakunan Fulani a karkashin Daular usmanniya ta Musulunci Sokoto Nijeriya Shehu idris shine ɗa na biyar a wajen mahaifiyarsa kuma ɗa na shida a cikin maza a wajen mahaifinsa. Shehu Idiris ya kasance shine mafi tsawon mulki a tarihin masarautar kasar Zazzau, ya kwashe tsawon shekaru 45 a sarautar.Ya hau karagar mulki tun a 8 ga watan Fabrairu shekarar alif 1975 biyo bayan rasuwar Sarkin Zazzau na goma sha bakwai Muhammadu Aminu a sanda Idris yake da shekaru 39 a rayuwarsa. Mahaifinsa shine Malam Idris Auta, mahaifiyarsa kuma itace Hajiya Aminatu Idris.[1].

Farkon Rayuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

Tarihin mai martaba sarkin zazzau Alhaji Shehu Idris ya fara ne daga 20 ga watan febrairu shekara ta 1936, wanda shine asalin ranan da aka haifawa malam Idrisu Autan Sambo da malama Aminatu matarsa ta uku. Bayan sati ɗaya da haihuwarsa an sanya ma yaron suna SHEHU USMAN kaman yadda addini da al’ada suka tanadar. An haifi Idris daga gidan malam Idrisu Auta wanda akafi sani da Auta Sambo taré da matarsa Hajiya Aminatu.[2].[3]

Karatu[gyara sashe | Gyara masomin]

Shehu ya fara karatu yana ɗan shekara biyar. A wannan shekarun ba’a aika shi makarantar nursery ko firamari ba sai dai an tura shi makarantar islamiyya inda ya koyo karatun Al-Qur’ani kamar yadda addini ya tanadar. Shehu ya kasance ɗalibi mafi ƙwazo a lokacinda yake zuwa makarantar allo, saboda baya taɓa yin fashin ajin safe ko na yamma,ba tare da wani dalili mai karfi ba.Ranaku biyar ne ake zuwa makarantar a sati watau daga Asabar zuwa laraba karfe 7:30 zuwa 11:30 da safe, sai kuma 2:30 zuwa 6:00 da yamma.[4] A lokacin da ya kai shekara 11 an sanyashi makarantar zamani a nan garin Zaria  a shekarar 1947. Dukda yana zuwa makarantar boko domin neman ilimin zamani, hakan bai hana shi cigaba da karatunsa na addini ba.[4].

Masarautar Zazzau 01.jpg

Sarauta[gyara sashe | Gyara masomin]

Shehu Idris ya zama Sarki ne sanda Jihar take amatsayin Jihar Arewa ta Tsakiya a shekara ta 1975. A shekarar mai zuwa, Janar Murtala Mohammed lokacin yana Shugaban kasa ya canja mata suna zuwa Jihar Kaduna. Bayan an kwashe shekaru goma sha daya, sai Janar Ibrahim Babangida ya raba jihar zuwa gida biyu Katsina da Jihar Kaduna a shekara ta1987. Inda rabewar ya haifar da natsuwa akan tashin hankalin dake faruwa tsakanin Masarautar Katsina da ta Zazzau a sanda suke jiha daya. Amma dukda wancan rabewar kuma, sai aka sake samo wata sabuwar rabuwa tsakanin mutanen dake rayuwa a kudancin Kaduna da Arewacin Kaduna.[5][6] Idris yafara karatunsa ne daga samun koyarwa na addini a wurin malamai a Zaria da Kuma cigaba da makarantar Zaria Elementary School.[7] Yana elementary school dafa 1947 zuwa 1950, Inda a wannan lokacin ya rasa mahaifinsa yana da shekara 12.[7] Idris ya cigaba da karatun alkur’ani da na zamani har yakai ga Zaria Middle School a 1950 sa'annan ya kammala karatunsa a 1955.[7] Sannan ya shiga Katsina Training College inda yazama malamin makaranta mai koyarwa.[3]

Wanda wannan rabuwa ta haifar da rashin jituwa da dama. Wadanda suka shahara sune Rikicin Kafanchan a 1987, Fadan Zangon Kataf sau biyu a 1992, fadan Shari’a a 2000 da kuma fadan bayan zaben shekara ta 2011 da 2012. Lokacin sarautar Shehu Idris, yawancin dukkanin yankunan alummu dake cikin garin Zazzau wadanda ba Hausawa ba an basu cin gashin kansu kuma suka zama Masarautun kansu. Wannan yakamata ya bakanta ma Idris rai. Biyo bayan kirkiran wata sabuwar masarauta a 2001, wasu bangaren Musulmai dake Zazzau suma sun nemi a basu cin gashin kansu. Samun kaiwa shekaru 45 a sarauta ba karamin abu bane, Kuma yazamo mafi tsawon mulki a tarihin sarautar Zazzau.

A yan' wannan karnin, an sha samun tsige-tsigen sarakunan gargajiya a masarautun Arewacin Najeriya. Sultan Ibrahim Dasuki an tsige shi a 1996; sarkin Gwandu Almustapha Jokolo an tsige shi a 2005 da Kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II shi ma an tsige shi a farkon shekarar 2020. Haka Kuma sarakunan a Muri, Suleja da Agaie. Sai dai Sarkin Zazzau ya kiyaye wa kansa duk wani abunda zai sanya asamu matsala tsakanin shi da wani Shugaba.

Aiki[gyara sashe | Gyara masomin]

Idris nada shekaru 39 ne asanda ya zama Sarkin Zazzau a watan Febrairu na shekara ta 1975. Gabanin hawan sa sarauta ya kasance hakimi Kuma malamin makaranta. Gwamnan Kaduna na wancan lokaci Birgediya Abba Kyari shine ya nada Shehu Idris amatsayin Sarkin Zazzau na sha takwas a shekara ta 1975.

Shehu Idris a makarantar sakandiri

Dangi[gyara sashe | Gyara masomin]

Shehu shine ɗa na biyar a wajen mahaifiyarsa kuma ɗa na shida a cikin maza a wajen mahaifinsa. Shehu karami ya kasance kyauta ne mai matuƙar rahama daga Allah wanda iyayensa suka yiwa Allah godiya akan samunsa da suka yi.[8] Shehu Idris ya taso ne a gidan yawa saboda mahaifinsa yana da mata har guda huɗu , kuma gidan ya kasance daga sashin mulkin katsinawa a zazzau. Shehu ya samu tarbiyya kai tsaye daga wajen iyayensa malam Idris Autan Sambo da malama Aminatu tare da taimakon sauran iyayensa mata na gida. Malama Suwaibatu, Malama Zainabu, Malama Raliyatu. Kuma dukkanin su sun karkatu ne akan tarbiyya ta addini da kuma al’adu na ƙwarai. Al’ada ne a ƙasar hausa uwa take ɓoye sunan ɗanta na farko ko na biyu saboda alkunya, amma malama Aminatu ta ɓoye gabadaya sunayen yaranta guda biyar inda kowanne ta bashi laƙabi da take kiransa da shi, ya kasance shehu ya samu suna “Na Allah”. Kuma ta kanyi wasa dashi a matsayin yaronta na biyar.[8] Shehu karami ya kasance kyauta ne mai matuƙar rahama daga Allah wanda iyayensa suka yiwa Allah godiya akan samunsa da suka yi.[9]

Mutuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

A yanzu bayan rasuwa Alhaji Shehu Idris gasar data dade a kwance ta tashi tsakanin a wane gida ne Sabon sarki zai fito,Barebari,Mallawa, Sullubawa ne ko kuma daga gidan Shehu Idris’Katsinawa. Yarimomi sun daɗe tsawon shekaru 45 suna jiran wannan damar.

Hotuna[gyara sashe | Gyara masomin]

Bibilyo[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Dalhatu, Ibrahim. Alhaji Shehu Idris, the 18th fulani emir of zazzau. Hassan, Musa. ISBN 978-2118-028

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. https://dailytrust.com/history-beckons-as-emir-of-zazzau-marks-45th-anniversary
  2. "Emir Shehu Idris of Zazzau: Exit of a gentleman peacemaker". www.pressreader.com. Retrieved 21 September 2020.
  3. 3.0 3.1 Marshal, Adamu (14 January 2015). "HH Alhaji Shehi Idris". Kabidonews.com. Retrieved 30 April 2016.
  4. 4.0 4.1 Dalhatu, Ibrahim. Alhaji Shehu Idris,the 18th fulani emir of zazzau. Hassan, Musa. p.p. 60-63 ISBN 978-2118-028
  5. "Zazzau Emirate Council Member shot dead in Kaduna". Premium. Retrieved 10 November 2015.
  6. "I Owe Long Life, Peaceful Coexistence To Almighty Allah – Shehu Idris". Leadership Newspaper. Archived from the original on 9 September 2015. Retrieved 10 November 2015.
  7. 7.0 7.1 7.2 "The Emir of Zazzau, His royal Highness Alh(Dr) Shehu Idris, is dead". NewsWire NGR. Retrieved 21 September 2020.
  8. 8.0 8.1 Dalhatu, Ibrahim. Alhaji Shehu Idris, the 18th fulani emir of zazzau. Hassan, Musa. p.p. 57-59 ISBN 978-2118-028
  9. Dalhatu, Ibrahim. Alhaji Shehu Idris, the 18th fulani emir of zazzau. Hassan, Musa. p.p. 57-59 ISBN 978-2118-028