Sanusi Lamido Sanusi
|
| |||||||
23 Mayu 2024 - ← Aminu Ado Bayero
8 ga Yuni, 2014 - 9 ga Maris, 2020 ← Ado Bayero - Aminu Ado Bayero →
3 ga Yuni, 2009 - 20 ga Faburairu, 2014 | |||||||
| Rayuwa | |||||||
| Haihuwa | jahar Kano, 31 ga Yuli, 1961 (64 shekaru) | ||||||
| ƙasa | Najeriya | ||||||
| Ƴan uwa | |||||||
| Mahaifi | Aminu Sanusi | ||||||
| Karatu | |||||||
| Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello King's College, Lagos | ||||||
| Sana'a | |||||||
| Sana'a | Ma'aikacin banki da Malami | ||||||
|
Mahalarcin
| |||||||
| Imani | |||||||
| Addini | Musulunci | ||||||
[Fayil:Emir Muhammad Sanusi II with US Special Rep to Muslim Communites, Shaarik H Zafar 2.jpg|thumb|Sarkin Kano Muhammad Sunusi 2 Da US Special Rep to Muslim Communites, Shaarik H Zafar]
Sanusi Lamido Sanusi
Sanusi Lamido Sanusi (Taimako·bayani) (An haife shi a ranar 31 ga watan Yuni, alif ɗari tara da sittin da ɗaya shekara ta (1961)[1] miladiyya Isa ɗan Maryam. Ɗan gidan sarautan Kano ne kuma tsohon Shugaban babban bankin Nijeriya (CBN)[2]. A yanzun sarkin Kano na 14 da Kuma na 15. An naɗa shi sarauta ne a ranar takwas ga watan Yuni na shekara ta dubu biyu da goma sha huɗu, 2014 bayan rasuwar tsohon sarkin [Kano (birni)|Kano] Ado Bayero.[3] Zuwa 9 ga watan march shekara ta dubu biyu da ashirin, 2020. Sarki Sanusi ma'aikacin banki ne, wanda shine tsohon Shugaban Babban Bankin Nijeriya[4]. Wanda ya riƙe muƙamin tun daga uku (3) ga watan Yuni na shekara ta dubu biyu da tara, 2009, da yayi tsawon shekara biyar akai, kamar yadda dokar muƙamin ya tabbatar amma sai dai Sanusin bai cika shekarunsa ba inda tsohon shugaban ƙasa na waccan lokaci, wato Goodluck Jonathan[5] ya tsige shi a ranar ashirin ga watan February shekara ta dubu biyu da goma sha huɗu, 2014, sanadiyar Sanusi ya bankaɗo wani zargi na badaƙalar kuɗi $20 billion a hukumar matatar man fetur na ƙasa (NNPC).



Sanusi jika ne na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, Sarki na 11th cikin sarakunan Fulani Na Kano.[6] Ma'aikacin banki ne kuma babban mutum ne, Malamin addinin musulunci ne da ake girmamawa.[7] Tun bayan sauƙe sarkin Kano Sanusi na II da gwamnatin jahar ta yi daga sarautar Kano, inda ya koma jihar Legas da zama, tsohon sarkin ya kai ziyarar sa ta farko a jihar Kaduna a ranar 23 Augusta 2020. Inda yazo dan girmama aikin da gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai[8] ya bashi tun bayan sauke shi daga kujerarsa.[9]
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ta 2024 bayan da majalisar dokoki ta soke dukkan masarautun jihar biyar da aka ƙirƙira a shekarar 2019.[10]
Jim kaɗan bayan rattaba hannu a kan dokar, gwamnan ya sanar da naɗa Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano na 16, bayan ya sauke Aminu Ado Bayero daga kan kujerar.[11]
Matakin kuma ya nuna cewa an soke masarautun Gaya da Bichi da Ƙaraye da kuma na Rano.[12]
Shekaru huɗu da suka wuce ne gwamnan Kano na wancan lokacin, Abdullahi Umar Ganduje ya cire Muhammadu Sanusi II daga sarautar Kano bisa dalilan da suka haɗa da 'rashin biyayya' ga gwamnati.[13]
Tun bayan da gwamnatin jam'iyyar APC ta sha kaye a zaɓen gwamna a 2023, lamarin da ya bai wa jam'iyyar NNPP damar kafa sabuwar gwamnati, masu sharhi suka soma bayanai a kan cewa Muhammadu Sanusi zai iya komawa kan kujerarsa.[14]
Sannan kuma makomar sabbin masarautun da aka ƙirƙira zai fuskanta cikas. Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin Khalifa Muhammadu Sanusi da kuma jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na tsawo shekaru. Kwankwaso ne ya naɗa Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14 bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero ƴan watanni bayan da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya cire Sanusi a matsayin gwamnan babban bankin ƙasar. A farko shekarar 2024 ne maganar sake dawo da Sanusi kan karagar mulki ta soma fitowa fili bayan da Sanata Rabiu Kwankwaso ya tabbatar wa manema labarai cewa za a sake nazari a kan dokar da ta kafa sabbin masarautun Kano.[15]
"Dole za a zo a yi magana, a duba a ga abin da ya kamata a yi a kai, gyara za a yi ko rusau za a yi," in ji Kwankwaso. Waɗansu masu sharhi sun ce tun lokacin kamfe, Sanusi ya nuna goyon bayansa ga Abba Kabir Yusuf kuma duk makusantar Khalifan Tijjaniyar sun goyi bayan jam'iyyar NNPP ta kafa mulki a jihar Kano. Hakan ya sa masu sharhi da dama suke ganin cewa dama lokaci kawai ake jira domin a rama wa kura aniyarta. Dr Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta CAS a Kano kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya ce akwai waɗanda za su iya ganin cewa alaƙar Sanusi da Kwankwaso ce ta sa aka mayar da shi kan mulki.[16]
"Akwai waɗanda za su iya ganin hakan ta wani ɓangaren za a iya cewa haka ɗin ne, tun da buƙata ta haɗe a wuri ɗaya, sannan kuma duk an taimaka wa juna. Yanzu za a iya cewa wataƙila an tasamma yin haka ɗin ke nan ko kuma an tasamma rama wa kura aniyarta ne," in ji Sufi.[17]
Shin kana ga tafiyar za ta ɗore? Maganar da mutane da dama suke ta yi ke nan. Sai Dr Kabiru Sufi ya ce "za ta iya ɗorewa kuma za ta iya samun matsala. Ya danganta ga abubuwan da suka biyo baya da kuma yadda dukkanin ɓangarorin suka karɓi al’amarin. Wannan hasashe ne da ba za a iya cewa ba. Wataƙila idan ɓangare ɗaya yayi haƙuri, to tafiyar za ta iya yin tsayi". "Amma kuma idan ya kasance aka samu akasin hakan, ya danganta da yadda ɓangarorin guda biyu ko kuma dukka waɗanda ke cikin al’amaran musamman sabuwar tafiya ɗin. Ya danganta ga yadda suka yi matsayin nasu shi ne zai sa a samu tsawo ɗin ko kuma a samu akasin hakan," in ji Sufi.[18]

Tsige shi
[gyara sashe | gyara masomin]Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje a ranar 9 ga watan maris shekara ta dubu biyu da ashirin, 2020 ya sauke shi daga kan karagar mulki.[19] [20]
Gwamnatin ta bayyana wasu dalilai dayasa suka sauke shi daga kan Mulki, dalilan sun haɗa da:[21]
- Rashin Biyayya;
Rashin halartar tarukan da gwamnati ke gayyatarsa ba tare da bada kwakkwaran dalili ba “Hakan rashin biyayyane,” inji sanarwar gwamnatin.
- Kare mutuncin Kano;
Kare mutuncin al`ada da addini gami da kimar masarautar mai dadadden tarihi wacce aka kafa ta shekaru dubbai da suka shude na daga cikin dalilan da suka sa aka dau matakin sauke sarkin. Inji sanarwar.
- Sukar manufofin gwamnati;
Sarkin ya soki shirin gwamnatin jahar na ciwo bashi daga kasar chaina domin aiwatar da gina layin dogo a cikin birnin na kano yasa wasu da dama ke ganin na daga cikin dalilan da yasa aka sauke tsohon sarkin.
Dawo da Sanusi a Matsayin Sarkin Kano
[gyara sashe | gyara masomin]Gomnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake tabbatar da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sarkin Kano. Ayau Alhamis 23 ga watan Mayu, shekarar 2024. Bayan Majlisar jihar ta kano ta sauke dokar da tsohon Gomna Abdullahi Umar Ganduje. Wanda ya maida masarautar guda biyar (5).[22]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.bing.com/ck/a?!&&p=74563325a9e3fb03JmltdHM9MTcxOTAxNDQwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTI3OQ&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Sanusi+Lamido+Sanusi+biography&u=a1aHR0cHM6Ly93d3cuZW50cmVwcmVuZXVycy5uZy9zYW51c2ktbGFtaWRvLXNhbnVzaS8&ntb=1
- ↑ https://www.bing.com/ck/a?!&&p=03d9bf696f2f541bJmltdHM9MTcxOTAxNDQwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTI0Mg&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Sanusi+Lamido+Sanusi+cbn&u=a1aHR0cHM6Ly93d3cuY2JuLmdvdi5uZy9hYm91dGNibi9UaGVCb2FyZC5hc3A_TmFtZT1NciUyRStTYW51c2krTGFtaWRvK1NhbnVzaSslMjhDT04lMjkmQmlvZGF0YT1sYW1pZG8&ntb=1
- ↑ http://www.nigerianbiography.com/2015/10/biography-of-sanusi-lamido-sanusi.html[permanent dead link]
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://punchng.com/13-states-show-inflation-slowdown-as-cbn-policy-takes-effect/%3Famp&ved=2ahUKEwjn9qnd7_GGAxXSVUEAHat6CskQyM8BKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw2qk8O7jZnLVUCRWqU_Ovgy
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.thisdaylive.com/index.php/2024/06/19/at-goodluck-jonathans-dialogue-bauchi-gov-canvasses-integrity-vision-in-africas-governance/&ved=2ahUKEwi9zviB8PGGAxUHX0EAHUkhJq0QxfQBKAB6BAgREAI&usg=AOvVaw0U2bypDEhcXKsrASAWmryE
- ↑ "Mr. Sanusi Lamido Aminu Sanusi". Central Bank of Nigeria.
- ↑ "The Role of Islam in Nigeria". The University of Georgia.
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/pidgin/articles/cp00j24ym55o.amp&ved=2ahUKEwiv7dPp8PGGAxViVEEAHZxpCiUQyM8BKAB6BAgLEAI&usg=AOvVaw1UADBSMBC0QxgS0OrM0WzP
- ↑ https://news-af.feednews.com/news/detail/e000c9371ed4f08ef484ce3461ad6a64?client=news
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ bbc
- ↑ bbc
- ↑ https://dailypost.ng/2020/03/09/breaking-emir-of-kano-muhammadu-sanusi-dethroned/
- ↑ https://www.bbc.com/news/world-africa-51804764
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-51803542
- ↑ https://leadership.ng/breaking-gov-yusuf-confirms-leadership-story-reinstates-sanusi-ii-as-kano-emir/?utm_source=dlvr.it&utm_medium=twitter
. . . . . . .
- All articles with dead external links
- Articles with dead external links from December 2024
- Articles with invalid date parameter in template
- Articles with permanently dead external links
- Mukaloli masu sauti
- Sarakunan Kano
- Sarakunan Nijeriya
- Mutanen Nijeriya
- Yan'siyasan Najeriya
- Gwamnonin Babban bankin Najeriya
- Rayayyun mutane
- Fulani
- Haifaffun 1961
- Mutane daga jihar kano
- Maza