Nasir Yusuf Gawuna
Nasir Yusuf Gawuna | |||
---|---|---|---|
2015 - 29 Mayu 2023 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | jahar Kano, 6 ga Augusta, 1967 (57 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Nasir Yusuf GawunaNasir Yusuf Gawuna (Taimako·bayani) (An haife shi ranar 6 ga watan Agustan, shekara ta alif ɗari Tara da sittin da bakwai 1967 A Unguwar Gawuna ƙaramar Hukumar Nasarawa dake cikin kwaryar birnin Jihar Kano. Shi ma’aikacin lafiya ne, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wanda shine Mataimakin Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje. Yayi takarar zama gwamnan Jihar Kano a Zaben Gwamnan Jihar Kano na shekarar dubu biyu da ashirin da uku (2023) karkashin jam'iyyar APC inda yayi rashin nasara a Hannun Abba Kabir Yusuf.A ashirin 20 ga watan September kotun sauraron kararrakin zabe ta ayyana gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gomnan kano[2]
Rayuwar farko
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Nasir Yusuf a ranar shida 6 ga watan Agustan shekara ta alif Ɗari Tara da sittin da bakwai 1967 a unguwar Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nassarawa ta jihar Kano
Harkar siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]An naɗa Nasir Yusuf Gawuna ne wanda Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada bayan murabus ɗin da tsohon Mataimakin Gwamna Farfesa Hafiz Abubakar[1] a ranar 5 ga watan Agustan shekara ta 2018, Gwamna Ganduje ya kuma rike Gawuna a matsayin abokin takarar sa a babban zaben Najeriya na 2019. kafin nadin nasa Gawuna shi ne Kwamishina a Kano, na Ma’aikatar Aikin Gona, tun a shekara ta 2014 aka fara nada shi a matsayin kwamishina daga tsohon Gwamnan Kano Injiniya Eng Rabi'u Musa Kwankwaso.
Gawuna ne shugaban Kano Taskforce kwamitin on Covid-19
Ya kasance shugaban karamar hukumar Nassarawa na tsawon shekaru 8 a karkashin rusasshiyar jam’iyyar All Nigeria Peoples Party ANPP yayin da Ibrahim Shekarau ya kasance Gwamnan Kano, yayi aiki tare da dukkan Gwamnonin Kano 3 tun daga shekarar alif 1999 zuwa yanzu.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Majalisar Zartarwa ta jihar Kano
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]2)Shafin BBC Hausa. wallafar Abubakar Sidi.