Jump to content

Kasuwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
kasuwa
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na market (en) Fassara, wuri da wuri
Bangare na Brazilian cuisine (en) Fassara
Hashtag (mul) Fassara Wochenmarkt da Market
wata babban kasuwa mutane nata kaida-kawo suna saye-saye
mutane na cin kasuwa
wata babban kasuwa anata hada-hadar kasuwanci
an kasa kayan marmari a kasuwa
Kasuwan kifi
wata kasuwa

Kasuwa, wani keɓantaccen guri ne da ake tanada don haɗuwa a yi cinikayya wato saye da sayarwa. Gurin hada-hadar kasuwanci [1] Wanda ita kasuwa tana haɗa mutane daban-daban daga wurare mabam-banta da ƙasashe daban-daban kuma ita kasuwa kusan komai akwai a cikinta. Jam'in kasuwa shi ne kasuwanni haka kuma wanda yake harkar.

kasuwanci ana ce masa ɗan kasuwa. Ana yi wa kasuwa kirari da "kasuwa akai maki tilas in an ƙiya a kai maki babu" kasuwanni iri-iri ne akwai kasuwar dabbobi akwai kuma kasuwar hatsi da dai sauran kasuwanni. Akwai kasuwa da ake cinikayya ta cikin ƙasa akwai kuma ta ƙasa da ƙasa.[2]

Bunƙasa Tattalin arziki

[gyara sashe | gyara masomin]

Kasuwa dai baya ga bunƙasa tattalin arzikin waɗanda ke yin kasuwancin, tana kuma bunkasa ko taimaka wa gwamnati ta hanyar samun kuɗaɗen shiga ta sigar biyan haraji daga `yan kasuwa. Akan bayar ko haraji a duk sati ko wata ko kuma ya danganta da yadda gwamnati ta tsara za ta rinka amsa a lokacin da ta tsara.