Dimokaradiyya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Dimokaradiyya (fasarar “mulkin talakawa”), amma yanzu, tsari ne gwamnati wanda ýan 'Kasa na mulki ko su za'bi wakilai a tsakaninsu domin su kafa hukumar gudanarwa, kamar majalisar dokokin dimokaradiyya an fara ta ne a 'Kasar Girika wanda wakilan ýan siyasa da aka zaba daga shaidun Kotu tsakanin ýan 'Kasa maza masu arziki da talakawa.

Bisa ga mai ilimin siyasa Larry Diamond, dimokaradiyya tana da abubuwa hudu: (a) hanyar siyasa don zabe da kuma maye gurbin gwamnati ta tsarin zaben adalci da gaskiya; (b) gudumawar jamaá a matsayinsu na ýan 'Kasa cikin siyasa da ýancin rayuawa; (c) kariyar ýancin 'dan Adam na dukan ýan 'Kasa da (d) mulkin doka, wanda dokoki da hanyar da za a zatas da su dai-dai ga dukan ýan kasar.

A karni na biyar (5) kafin haifuwar Annabi Isah, a biranen tarayya ta Girika, an nuna tsarin siyasa wanda an fi sani da Athens, dimokaradiyya akasin sarauta ne,wato, 'mulkin dan yawa'. A rubuce wadannan bayanai akasin dimokaradiyya ne kuma an kauce wa manufar dimokaradiyya bisa ga tarihi. Tsarin siyasar Athens ta ba ýan Kasa ýanci mai adalci da su yantar da maza wajen siyasa, barori ba su da wannan ýancin shigar siyasa. A tarihin gwamnatin dimokaradiyya na dá da na zamani, zama dan wakili mai adalci ta kunshi yardan jamaá bayan an ci ainihin zabe da manyan mutane sun yi bisa ga yawancin siyasan yau bisa ga zaben raáyi a karnin 19 da na 20. Turai ta fara daga karni na 16, daga tsohowar tsakar Faransa da tsakar Latin.

An kwatanta dimokaradiyya da siffar gwamnati inda mutum daya ke da iko kamar ta mulkiya ko ikon kalilar mutane. Duk da haka, wadannan hamayyar da an gada daga mai ilimin falfasa na Girika na baki-biyu sabida gwamnatin yanzu na da siyasar hántsuná, mulkin kalila da ababan mulukiya. Mai suna Karl Popper, ya bayyana Dimokaradiyya da kwatanci da mulkin kama karya ko zalunci, da sa hankali ga damar damar jamaá da su jagoranci shuwagabanensu da su hambarar da su ba tare da bukatan juyin mulki ba.