Ahmadu Bello

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Ahmadu Bello
Rayuwa
Haihuwa Rabbah (en) Fassara, 12 ga Yuni, 1910
ƙasa Najeriya
Mutuwa Kaduna, 15 ga Janairu, 1966
Yanayin mutuwa kisan kai
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Northern People's Congress (en) Fassara
Firimiyan Lardin Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto
Jami'ar Ahmadu bello
Ahmadu bello sardauna tare da wasu mutane

Sir Ahmadu Muhammadu Bello KBE ko Sardauna shine tsohon Firimiyan Arewacin Nijeriya kuma yarike sarautar Sardaunan Sokoto. An haifi Ahmadu Bello a garin Raba dake cikin lardin Sokoto a shekara ta alif dubu daya da dari tara da goma (1910). A shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da tara 1949 ya sami zuwa majalisar dokoki ta jihar arewa, yana kuma daga cikin mutum na uku da aka zaba acikin kungiyar da ta rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar.[1] Sardauna yakasance wani mutumi ne dake da mahimmanci sosai ga mutanen arewacin Najeriya, da ma padin kasar gaba daya, saboda irin ayyukan cigaba daya kirkira a yankin arewa harma da kudancin kasar gaba daya. Kamar jami'ar Ahmadu Bello, Gidan Rediyo dake jihar Kaduna, da sauransu. Duk da cewa Sardaunan sokoto Sarauta ce tashi a jihar sokoto, Amma sunan ya zama kamar wani inkiya a gareshi inda ya shahara wajen amsa shi.

Farkon Rayuwarsa[gyara sashe | Gyara masomin]

Ahmadu Bello Sardauna An haife shi a garin Raba, shekara ta alif dubu daya da dari tara da tara (1909), a Gidan Mallam Ibrahim Bello. Mahaifinsa shine Sarkin Raba.[2] kuma zuri'ar Usman Dan Fodio ne, kuma tattaba kunnen Sultan Muhammad Bello kuma jikan Sultan Atiku na Raba. Yayi makarantar Sokoto Provincial School da kuma Katsina Training College. Lokacin karatun sa ansansa da Ahmadu Raba.[2] ya kammala karatu a shekara ta alif dubu daya da dari tara da talatin da daya (1931), sannan yazama babban Malamin harshen turanci a Sokoto Middle School.

Mafarin Siyasarsa[gyara sashe | Gyara masomin]

Ahmadu bello sardaunan sokoto da sa'adu alanamu da kuma wani mutumi

A shekara ta alif duubu daya da dari tara da talatin da hudu (1934), an nada Ahmadu Bello hakimin garin Raba daga Sultan Hassan dan Mu'azu, inda yagaji dan'uwansa. A alif dubu daya da dari tara da talatin da takwas (1938), an masa Karin girma a matsayin Shugaban Gusau dake jihar Zamfara ayau. kuma yazama mabiyi a masarautar Sultan's council. A alif dubu daya da dari tara da talatin da takwas (1938), yanada shekara 28, yayi kokarin zama Sultan of Sokoto amma baisamu nasara ba, yasha Kaye a hannun Sir Siddiq Abubakar II wanda yayi mulki na tsawon shekaru hamsin (50), har sai sanda yarasu a alif dubu daya da dari tara da tamanin da takwas(1988). Sai sabon Sarkin yayi maza yanada Sir Ahmadu Bello da Sardaunan Sokoto, sarautan girmamawa kuma yakaisa ga matsayin Sokoto Native Authority Council. Wadannan mukaman ne suka kai shi har ya zama babban mai bawa sultan shawara akan har kokin siyasa. Daga bisani, aka bashi ikon duba gundumomi arba'in (47) daga alif dubu daya da dari tara da arba'in da hudu (1944), ya dawo fadar maimartaba Sultan danyin aiki a matsayin babban mai kula da jaha akan al-amuran da gargajiya (Chief Secretary of the State Native Administration).

A kuma shekarun alif dubu daya da dari tara da arba'in (1940s), sai ya shiga cikin Jam'iyyar Mutanen Arewa wanda daga baya takoma NPC a 1951. A 1948, yasamu tallafin karatu daga gwamnati zuwa kasar England Dan yin karatun Local Government Administration wanda yakara masa karin ilimi da fahimtar gwamnati.

Bayan dawowarsa daga Britain, an zabeshi ya wakilci yankin Sokoto a regional House of Assembly. A matsayinsa na member of the assembly, yakasance Dan rajin hakkin arewacin Najeriya da kuma hadin kan wakilan yankin wadanda suka fito daga manyan masarautun arewa, wato Kano, Masarautar Borno da Sokoto. An zabeshi da wasu a matsayin member of a committee wadanda sukayi Richards Constitution kuma yaje general conference a Ibadan. Aikin sa a assembly da kuma gun tsarin constitution drafting committee yajanyo masu yarda da kauna a arewa, hakane yasa aka zabe shi da yayi mulki a karkashin Jamiyyar Mutanen Arewa.[2] A zabukan da aka gudanar na farko a arewacin Najeriya a 1952, Sir Ahmadu Bello yasamu nasarar zuwa e Northern House of Assembly, kuma yazama member of the regional executive council as minister of works. Bello yarike ministan ayyuka, dana Local Government, da of Community Development in the Northern Region of Nigeria. A 1954, Bello yazama Premier na farko a Northern Nigeria. A kuma shekara ta 1959 a zabukan yancin kai, Bello yajagoranci jamiyar NPC harta samu nasara da yawan kujeru a majalisar kasa. NPCn da Bello ke jagoranta ta kulla kawance da jamiyar Dr. Nnamdi Azikiwe NCNC (National Council of Nigeria and the Cameroons) to form Nigeria's first indigenous federal government which led to independence from Britain. In forming the 1960 independence federal government of the Nigeria, Bello a matsayinsa na shugaban NPC, yazabi tacigaba da zama Premier na Arewacin Nijeriya sannan yabayar da matsayi.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. http://www.dw-world.de/dw/article/0,,2846635,00.html
  2. 2.0 2.1 2.2 cite news |last=Savage |first=Babatunde |date=1959-03-16 |title=Profile of a Fearless Leader |url= |newspaper=Daily Times |location=Lagos |access-date=