Masallacin Sarkin Musulmi Bello
Masallacin Sarkin Musulmi Bello | |
---|---|
Wuri | |
Coordinates | 10°33′03″N 7°26′45″E / 10.5508°N 7.4458°E |
History and use | |
Opening | 1962 |
|
Masallacin Sarkin Musulmi Bello (da Turanci Sultan Bello Mosque, da larabci مسجد سلطن بلو) ana kuma kiran sa da Babban Masallacin Kaduna, wato Kaduna Central Mosque, shi ne Masallaci mafi girma a Jihar Kaduna, Nijeriya, an gina shi a shekarar 1962. Masallacin yana a Unguwar Sarki Kaduna. Ansa masa sunan tsohon Sarkin Musulmi wato, SarkiMuhammadu Bello ɗaya daga cikin yayan Shehu Usman dan Fodiyo. Babban limamin Masallacin shine Sheikh Suleiman Muhammad Adam.[1][2] Wanda tsohon Malami ne a ɓangaren karatun Larabci da Addinin Musulunci a Jami'ar Jihar Kaduna.
Masallacin Sarki Bello ya samu aikin faɗaɗa shi daga asalin girman sa na faɗin 220m2 a sanda aka gina shi zuwa faɗi 2,300m2 a yanzu, kamar yadda yake. [3]An gina shine a shekarar 1962.
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Masallacin Sultan Bello ya kasance majalisi na karantar da al'umar musulmai, inda musulmai ke halartar masallacin domin ɗaukan karatu, a wannan masallacin ne marigayi Abubakar Gumi ke bada karatuttuka da yawa, a ciki har da Raddul azhan ila ma'anil qur'an, masallacin suna bin karantarwar Malikiyya ne, a yanzu haka babban ɗan sheikh Abubakar Gumi wato Ahmad Abubakar Gumi shike yin tafseerin alqur'ani duk shekara .
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Aerial View
-
Babbar hanyar shiga da kuma ƙofofi hudu na masallacin.
-
Hanyar shiga da fita.
-
Fuskar Masallacin daga yamma.
-
Hotun masallacin daga kan gada.
-
Gadar shiga masallacin.
-
Hanyar shiga masallacin.
-
Ga da ga
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Sultan Bello Mosque Gets new Imam"[permanent dead link] Daily Trust Kaduna, 22 November, 2017.
- ↑ Moh, Bello Zaria. " Zazzau Emir instals new Imam for Sultan Bello Mosque"[permanent dead link], Blueprint Newspaper, Zaria, Kaduna State.
- ↑ Archnet. "Sultan Bello Mosque Expansion". Cite has empty unknown parameter:
|1=
(help)