Jump to content

Suleiman Muhammad Adam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Suleiman Muhammad Adam
Rayuwa
Haihuwa 14 ga Yuni, 1962 (62 shekaru)
Sana'a
Dr Sulaiman Muhammad Adam

Dr. Sulaiman Muhammad Adam (An haife shi ranar 14 ga watan Yuni shekarar 1962), babban limamin Masallacin Sultan Bello dake unguwan sarki Kaduna a halin yanzu. Dakta Sulaiman ya fara jagorantar Sallar Juma'a a Masallacin Sultan Bello a ranar 6 ga watan Janairu shekara ta 2017.[1]

Sulaiman yayi karatun firamare a ƙauyen Umoko a Jihar Ribas, kudancin Najeriya. Bayan kammala karatun firamare sai ya zarce zuwa sakandare inda yayi Higher Islamic Studies (H I S) a Jos, a lokacin kuma ya shiga kwalejin Arabic Teachers College Grade 3. Daga nan kuma ya cigaba da karatunsa a kwalejin ilimi ta Kano, inda ya samu shaidar gama karatun NCE. Ya kuma samu shaidar digiri a Madina da kuma Maleshiya, inda ya karanta Larabci, Shari'a da kuma Ilimin Addinin Musulunci. Haka kuma tsohon Lakcara ne a Jami'ar Jihar Kaduna.[2]

  1. Ahmadu-Suka, Maryam (6 January 2017). "Suleiman Adam Is New Chief Imam Sultan Bello Mosque Kaduna". dailytrust.com (in Turanci). Retrieved 27 December 2023.
  2. "Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Sulaiman Sulaiman". BBC hausa.com. 13 January 2022. Retrieved 27 December 2023.