Ahmad Abubakar Gumi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Ahmad Abubakar Gumi
Abubakar Mahmoud Gumi.jpg
Rayuwa
Haihuwa Kaduna, 7 Nuwamba, 1959 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
ƙungiyar ƙabila Fulani
Yan'uwa
Mahaifi Abubakar Gumi
Karatu
Harsuna Turanci
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mufti (en) Fassara da Malamin addini
Imani
Addini Mabiya Sunnah
Malikiyya

Ahmad Abubakar Gumi (An haife shi 7 Nuwamba1959) Sannan fitaccen malamin addinin Islama ne a Nijeriya kuma mabiyin sunnah Malikiyya ne, Malami kuma tsohon jami'in sojan Najeriya ne wanda ya yi suna a matsayin kyaftin a Cibiyar horar da sojoji na Nijeriya wato (NDA), shi ne Mufti kuma mufassir yanzu haka a masallacin Juma'a na Kaduna, Sultan Bello .[1][2]

Farkon rayuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

Ahmad Gumi ɗan fari ne ga marigayi Shaykh Abubakar Gumi, an haife shi ne a jihar Kaduna.[3]

Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Ahmad Gumi ya halarci Kwalejin Sardauna Memorial College (SMC) don babbar sakandare, sannan aka shigar da shi Jami’ar Ahmadu Bello don yin karatun likitanci, bayan kammala karatun sa ya sa ya shiga Kwalejin Tsaron Najeriya . Gumi ya yi murabus daga aikin soja a matsayin Kaftin kuma ya koma Saudi Arabiya don ci gaba da karatunsa na Musulunci a Jami’ar Umm al-Qura inda ya yi karatun Islamiyya da Tafsiri . Abokan aikinsa a jami’ar sun hada da Abdur-Rahman As-Sudais, Saud Al-Shuraim . Hakanan yana bayar da Tafsirin Ramadan na shekara-shekara a Masallacin Sultan Bello Unguwan sarki Kaduna .

Aikin soja[gyara sashe | Gyara masomin]

Ya yi aiki a Kwalejin Tsaro ta Najeriya a matsayin jami'in soja, kuma ya yi ritaya a matsayin matsayin kyaftin.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. https://www.bbc.com/hausa/labarai-44699864
  2. https://dailypost.ng/2012/08/15/kaduna-blast-i-list-targeted-terrorists-sheikh-gumi/
  3. http://www.oxfordislamicstudies.com/Public/Login.html?url=/app?service=externalpagemethod&page=ArticleViewDispatch&method=view&uri=/opr/t343/e0059&failReason=Error+reason:+err_userpass_none+err_ip_badcred+err_athens_none+err_shib_none+err_referrer_badcred+err_libcard_none