Kabiru Gombe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Kabiru Gombe
Rayuwa
Haihuwa Yamaltu/Deba
ƙasa Najeriya
ƙungiyar ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malamin addini
Jagoranci Salafiyya
Imani
Addini Musulunci

Sheik Muhammad Kabiru Haruna Gombe

An haifi Malam a garin Kuri a karamar hukumar Yamaltu Deba,wacce take a jihar Gombe. Malam yayi makarantar firamare a garin Gombe, a islamiyya ta Izala anan garin Gombe Sheikh kabiru Gombe ya samu Haddar ALQUR'ANI mai girma tare da gyara karatun sa a wajen malamai irin su : Sheikh Zarma Gombe, Da Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan. Ya kuma yi wasu karatunsa na ilimi a wajen maluma irin su Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe. Sheikh Kabiru Gombe ya zama Alaramma mai jan baki a kungiyar Izala tun yana karami, kafin daga bisani ya juya zuwa mai wa'azi wanda a halin yanzu duniyar Hausa take amfana da wa'azin sa. Sheikh Kabiru Gombe bai tsaya iya wa'azi ba, yana taba kasuwanci sannan babban Manomi ne, Malam yana da mata hudu da yara da jikoki. Malam yana da baiwa kwarai, domin duk abun da malam ya haddace to da wuya kaga wannan abu ya salwanta a kwakwalwarsa Allah ya karawa rayuwar Sheikh albarka ameen.

Farkon rayuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

Da'awa[gyara sashe | Gyara masomin]

Zargi[gyara sashe | Gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]