Albani Zaria

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
StarIconGold.png Mukala mai kyau
Sheikh

Muhammad Auwal Adam
Title Albani Zaria
Personal
Haihuwa (1960-09-27)Satumba27, 1960
Mutuwa Fabrairu 1, 2014(2014-02-01) (shekaru 53)
St. Luke Hospital Zaria
Sababin mutuwa Kisan Kwangila
Addini Islam
Dan kasan Dan Najeriya
Kabila Hausa
Era Zamanin nan
Yanki Arewacin Najeriya
Reshan addini Sunna
Mazhabi Mazhaban da suka fi hujja
Dabbaga Salafiyya
Aiki mafi so Hadisi and Tafsiri
Babban tinani Qur'ani da Hadisi akan fahimtar magabata
Babban aiki Kawar da Bidi'ah da Kafa Salafiyyanci
Alma mater Jami'ar Ahmadu Bello
Darika baya ra'ayi
Sana'a Mai tafsiri, Malamin islama, Malami.
Muslim leader


Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria (An haife shi ne 27 ga watan Satumba shekarar 1960) Sannan ya rasu ne a 1 ga watan Fabrairu shekara ta 2014) ya kasance malamin addinin Islama ne a Najeriya wanda ya ƙware a fannin Hadisi. [1] Dokar Musulunci, kuma ya kware a Ilimin sadarwa kuma Injiniya ne, a fannin sadarwa ta zamani wato (ICT) . Kuma ya kasance Tela ne a matakin farko na rayuwarsa, wanda yake yawan kiran kansa da shi, wato (Kwararrun Teloli). Shine malami na farko da ya fara gabatar da kalmar da kuma akidar Salafiyyah ga tsirarrun daliban Islama a Najeriya. Malaman Najeriya da yawan su suna a wannan zamani suna ɗaukar shi a matsayin mafi girman malamin Salafiyyah a Najeriya . [2]

Farkon rayuwa da Ilimi[gyara sashe | Gyara masomin]

Albani ya samo asali ne daga jihar Kano a Arewacin Najeriya amma an haife shi ne a Muchia Sabon Gari, Zariya . Ya yi karatun farko a yankin kafin ya koma Kwalejin Barewa . Ya yi karatun Mass Communication a Jami’ar Bayero, Kano . Ya samu digiri a fannin Fasahar Sadarwa daga Jami’ar Fasaha ta Tarayya Yola, a Jihar Adamawa . Kafin rasuwarsa, ya nada a Digiri na biyu wato M.Sc a fannin injiniyarin din lantarki da injiniyarin din kayan wuta a ABU Zaria . Wannan baya ga babban karatunsa a cikin Sanin Addinin Musulunci musamman Hadisi, bayan da ya kwashe shekaru da yawa yana nazarin daruruwan littafan hadisi kuma yana koyarwa. Babban iliminsa da kuma ikonsa a Arewacin Najeriya ya sa ya karɓi suna na "Albani", an samo sunan ne daga shahararre Muhammad Nasiruddin al-Albani . Daliban sa, wadanda yawancinsu a yanzun malamai ne masu karantarwa, sun bazu a duk fadin kasar, musamman ma a jihohin Arewa musamman a jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Plateau, Bauchi da sauran Arewa da Kudancin Najeriya har ma da wasu kasashen Yammacin Afirka. . [3]

Da'awa[gyara sashe | Gyara masomin]

Mutuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

'Yan bindigar Boko Haram sun harbe Sheikh Muhamman Auwal Albani Zaria tare da daya daga cikin matansa a cikin garin Zariya a kan hanyarsu ta dawowa gida bayan sun halarci karatun Tafsirin yamma da suka saba zuwa a cikin garin. Matarsa ta mutu a daidai lokacin da aka harbe ta, a yayin da shi kuma aka garzaya da Sheikh zuwa asibitin St. Luka da ke yankin Wusasa a Zariya inda aka ce ya mutu. Jagoran Boko Haram mai suna Abubakar Shekau, ya dauki alhakin Kashe Sheikh Albani. [4] [5] [6]

Duba nan[gyara sashe | Gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. https://www.dailytrust.com.ng/the-man-sheikh-albani.html
  2. darulquranlitahfizilquran.blogspot.com/2014/08/history-of-albani-sheikh-muhammad-auwal.html?m=1
  3. https://nazeerdanjagale.wordpress.com/2016/09/07/short-biography-of-sheikh-albaniy-zaria/
  4. https://www.bbc.com/hausa/news/2014/02/140219_bokoharam_albani_responsiblity
  5. https://www.dailytrust.com.ng/the-assassination-of-auwal-albani.html
  6. saharareporters.com/2014/02/20/boko-haram-leader-claims-responsibility-killing-kaduna-cleric-sheik-albani-threatens