Jump to content

Albani Zaria

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukala mai kyau
Albani Zaria
Rayuwa
Haihuwa Zariya, 27 Satumba 1960
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Zariya, 1 ga Faburairu, 2014
Karatu
Makaranta Kwalejin Barewa
Harsuna Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a mufassir (en) Fassara da Ulama'u
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria (An haife shi ne a ranar ashirin da bakwai 27 ga watan Satumbar shekara ta alif dubu daya da sitting miladiyya 1960) Sannan ya rasu ne a ranar 1 ga watan Fabrairun shekara ta 2014) ya kasance malamin addinin Musulunci ne a Najeriya wanda ya ƙware a fannin Hadisi.[1] Dokar Musulunci, kuma ya ƙware a Ilimin sadarwa na zamani,kuma Injiniya ne a fannin sadarwa ta zamani wato (ICT). Kuma ya kasance Tela ne a matakin farko na rayuwarsa, wanda yake yawan ƙiran kansa da shi, wato (Kwararrun Teloli). Shi ne malami na farko da ya fara gabatar da kalmar da kuma akidar Salafiyyah ga tsirarrun daliban Islama a Najeriya. Malaman Najeriya da yawan su suna a wannan zamani suna ɗaukar shi a matsayin mafi girman malamin Salafiyyah a Najeriya.[2]

Farkon rayuwa da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Albani ya samo asali ne daga jahar Kano a Arewacin Najeriya amma an haife shi ne a Muchia Sabon Gari, Zariya. Ya yi karatun farko a yankin kafin ya koma Kwalejin Barewa. Ya yi karatun Mass Communication a Jami’ar Bayero, Kano. Ya samu digiri a fannin Fasahar Sadarwa daga Jami’ar Fasaha ta Tarayya Yola, a Jihar Adamawa . Kafin rasuwarsa, yanada Digiri na biyu wato M.Sc a fannin injiniyarin din lantarki da injiniyarin din kayan wuta a ABU Zariya. Wannan baya ga babban karatunsa a cikin Sanin Addinin Musulunci musamman Hadisi, bayan da ya kwashe shekaru da yawa yana nazarin ɗaruruwan littafan hadisi kuma yana koyarwa. Babban iliminsa da kuma ikonsa a Arewacin Najeriya ya sa ya karɓi suna na 'Albani', an samo sunan ne daga shahararran malamin Hadisi Wato Muhammad Nasuriddin Albani. Dalibansa, wadanda yawancinsu a yanzun malamai ne masu karantarwa, sun bazu a duk fadin ƙasar, musamman ma a jihohin Arewa musamman a jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Plateau, Bauchi da sauran Arewa da Kudancin Najeriya har ma da wasu kasashen Yammacin Afirka[3]

Yan bindigar sun harbe Sheikh Muhamman Auwal Albani Zariya tare da ɗaya daga cikin matansa a cikin garin Zariya a kan hanyarsu ta dawowa gida bayan sun halarci karatun Tafsirin yamma da suka saba zuwa a cikin garin. Matarsa ta mutu a daidai lokacin da aka harbe ta, a yayin da shi kuma aka garzaya da Sheikh zuwa asibitin St. Luka da ke yankin wusasa a Zariya inda aka ce ya mutu. Jagoran Boko Haram mai suna Abubakar Shekau, ya dauki alhakin kashe Sheikh Albani. [4] [5] [6]

Albani Zaria yace idan kana son najeriya ta gyaru to ka zama (Agent of change)

    • Kuma yace lallai ne chanji zai faru Kuma za,a chanja a Nigeriya
    • Saheehu Muslim 132
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-05-17. Retrieved 2019-09-29.
  2. darulquranlitahfizilquran.blogspot.com/2014/08/history-of-albani-sheikh-muhammad-auwal.html?m=1
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-05-17. Retrieved 2019-09-29.
  4. https://www.bbc.com/hausa/news/2014/02/140219_bokoharam_albani_responsiblity
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-05-17. Retrieved 2019-09-29.
  6. saharareporters.com/2014/02/20/boko-haram-leader-claims-responsibility-killing-kaduna-cleric-sheik-albani-threatens