Aikin Hajji
![]() | ||||
| ||||
Iri |
pilgrimage (en) ![]() | |||
---|---|---|---|---|
Bangare na | Rukunnan Musulunci | |||
Ƙasa | Saudi Arebiya | |||
Wurin masauki | Makkah | |||
Yana haddasa | Alhaji | |||
Hanyar isar da saƙo | ||||
Yanar gizo | hajinformation.com |

Aikin Hajji, Daya ne daga cikin rukunai guda biyar da aka gina addinin Musulunci a kai. Aiki ne a cikin addinin musulunci wanda Musulmi suke zuwa ƙasar Makkah, Saudi Arebiya domin aiwatar da waɗansu ibadoji. cikin ibadojin akwai Arfa, Safa da Marwa, Dawafi (zagayen Ka'abah ) Ziyarar Ma'aiki, Jifan Shaidan da dai sauran ibadu. Allah ya wajabta aikin hajji ga dukkan musulmin da Allah ya hore masa lafiya ta jiki da kuma amintacciyar hanya da kuma wadataccen guzuri, tare da samun muharrami ga wadda take mace ce ita.
Rabe-raben Aikin Hajji[gyara sashe | gyara masomin]
Hakika Aikin Hajji ya kasu zuwa kashi daban-daban har zuwa kashi uku, ga su kamar haka:
1 Hajj Tamattu'i Shi ne mutum ya yi niyyar umara a cikin watannin aikin hajji, ya gama umarar, ya fita daga cikin ihraminsa, sannan sai ya yi niyyar aikin hajji a wannan shekarar da ya yi umarar.
2 Hajj Qirani shi ne mutum ya yi niyyar hajji da umara a tare gaba ɗaya.
3 Hajj Al-ifrad Shi ne ya yi niyyar aikin hajji kawai.[1]