Kwa-kwa
| Kwa-kwa | |
|---|---|
|
tropical fruit (en) | |
|
| |
| Tarihi | |
| Mai tsarawa | Attagara |





Kwa-kwa, kwa-kwa wata bishiya ce daga cikin bishiyoyi wadda take da matuƙar amfani a jikin dan Adam [1] [2] [3] tana da magunguna sosai musamman man kwa-kwa [4] kuma bishiya ce mai tarihi sosai, kuma ana amfani da man kwa-kwa a fata[5] da kuma haɗa man kitso na mata da dai sauransu. Ana haɗa kwakwa da dabino don wasu magunguna[6]
Yawancin yankunan Najeriya suna da kyakkyawan yanayin da za a iya shukawa da samar da kwakwa.[7]
Amma duk da haka kasar na siyo kashi 70 cikin dari na wannan dan itace mai muhimmancin gaske da ake sarrafawa a yi abubuwa daban-daban, kama daga abin ci da abin sha da kuma man girki da na shafe-shafe.[8]
Ganin yadda bukatar kwakwa ke karuwa a cikin Najeriya da kuma kasashen duniya, yanzu akwai shirye-shirye na sa kasar ta zama mai dogaro da kai a fannin samar da kwakwar.[9]
A unguwar Isolo da ke tsakiyar babbar cibiyar kasuwanci ta Najeriya, wato Lagos, Toyin Kappo-Kolawole tana gudanar da wata ‘yar karamar masana’anta ta sarrafa kwakwa.[10]
Tana yin madara da ruwa da garin fulawa da kuma kayan kwalan da makulashe, duk da kwakwar.[11]
Ta fara gudanar da wannan kasuwancin nata ne inda ta sanya wa masana’antar suna De-Cribbs Cocogry Coconut, a 2018.[12]
Tana samo kwakwar daga garin Badagry, na gabar teku a jihar ta Lagos, inda nan ne aka fi samar da kwakawar a Najeriya.[13]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Maikatanga, Sani (1 March 2021). "Sirrin haɗa dabino da kwakwa da aya ga ma'aurata". bbc Hausa. Retrieved 3 July 2021.
- ↑ Daudawa Alyu, Idris (18 August 2019). "Hanyoyi Biyar Na Yadda Kwakwa Ke Amfani A Jikin Dan'Adam". leadership Ayau. Retrieved 3 July 2021.
- ↑ https://hausa.legit.ng/1238735-hana-tsufa-da-wasu-faidoji-10-da-ruwan-kwakwa-ke-dashi-a-jikin-dan-adam.html
- ↑ https://m.facebook.com/ciwodamagani/posts/1688090341310190
- ↑ https://m.facebook.com/permalink.php?story_fbid=214945486647902&id=112772390198546
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56199556
- ↑ Bbc
- ↑ Bbc
- ↑ bbc
- ↑ bbc
- ↑ Bbc
- ↑ bbc
- ↑ bbc