Karas

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Karas
root vegetable (en) Fassara, finger food (en) Fassara, food ingredient (en) Fassara, food crop (en) Fassara da taproot (en) Fassara
Tarihi
Mai tsarawa Daucus carota subsp. sativus (en) Fassara da Wild Carrot (en) Fassara
Karas bayan an wanketa
manya-manyan ƴaƴan karas
ganyen karas

Karas yana daga cikin tsirrai watau kayan da ake nomawa watau kayan lambu, kayan marmari kuma, kalarsa ja ce, amma ba ja sosai ba, sai dai an fi noma shi a noman rani. Karas na da amfani sosai, domin kuwa yana magunguna daban-daban. Ga wasu daga magungunan da karas ke yi: Maganin bugun zuciya, taimakawa Ido, cututtukan baki da haƙora, ƙarfafa ƙashi, da dai sauransu. [1]

Yadda ake noman Karas[gyara sashe | gyara masomin]

• Da farko dai ana yin kaftu, bayan an yi kaftu sai a yi kwami, bayan an yi kwami sai ban ruwa. Daga nan sai a shuka ta bayan kwana biyar da shuka ta zata fito (tsiro). Daga nan sai a yi ta ban ruwa, bayan wani ɗan lokaci kaɗan sai a zo a yi cira (za a cire ciyarwa dake cikin ta) daga nan kuma sai a sa mata taki. Shi karas aƙalla ba ta wuce wata uku (3) da shuka sai kuma ta yi, a fara ɗiban ta. [2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ibrahim, Aminu (25 January 2020). "Lafiya jari: Amfani 10 da karas ke yi a jikin dan adam". legit hausa. Retrieved 4 July 2021.
  2. Babanƙarfi, Aliyu (13 January 2020). "Noman rani a rafin Kubanni a gonar karas". Aminiya dailytrust. Retrieved 4 July 2021.