Bayajidda

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Bayajidda

An bayar da tarihi akan Bayajidda, a matsayin wani jarumi wanda yazo daga Baghdad, da farko ya sauka a Borno a inda aka aurar masa da diyar Sarkin Daular Borno wato Mai,sai yaji raɗe-raɗin cewa sarkin zai kashe shi ya gaje sojojinsa. Sai matarsa ta ce su gudu, sai suka gudu cikin dare. sa'annan daga bisani yatafi zuwa kasar Hausa, Ance ya sauka a garin Daura cikin dare a Gidan wato tsohuwa, inda kishirwa yakamata, ta bukaci yasamo mata ruwa, sai ya tambaye ta, a ina ne akwai rijiya? Sai ta gaya masa cewar akwai sarki(wani katon maciji dake hana a diba ruwa da daddare), amma Bayajidda bai tsorata ba, yaje rijiyar, Sarkin(Maciji) yafito ya nemi hana shi dinar ruwa, Bayajidda yayi fada dashi yasamu yakashe Sarki, kuma ya diba ruwarsa yakawo wa tsohuwa, ta cika da mamakin yadda yasamo mata ruwa acikin daren nan yakawo mata. Da gari yawaye, mutanen gari sunzo dibar ruwa, sai suka tarar da sarki a kwance, gashi ansare masa kai, al'umman gari suka fara murna da biki, cewar daga wannan lokaci babu abinda zai rika hanasu dibar ruwa, sai dai ba'asan wanda yayi wannan jaruntakar ba, har yasamu yakashe Sarkin, amma sai aka sama yamance da warin takalminsa kafa daya a gindin rijiyar. Sai Sarauniyar Daura tayi alkawarin bayar da rabin gari ga duk wanda yayi wannan jarunta, kawai dayan sawun takalminsa Dan a tabbatar, sai tsohuwa tazo ta bayar da labarin abinda yafaru da daddare, aka kira Bayajidda Sarauniya ta aurar masa da kanta, Bayajidda daga bisani tanada yaro da akekira "Bawo" da "Biram" daga matarsa Sarauniyar Borno, da kuma wani yaron "karbogari" daga kuyangarsa Bagwariya. Bawo ne yagaji mahaifinsa kuma yahaifa ya'ya shida(6), wadanda sune suka zama Sarakunan Daura, Katsina, Zazzau, Gobir, Kano da Rano. Wadannan, tareda Biram, wadda Shugaban ta shine dan Bayajidda daga wurin matarsa Sarauniyar Borno, sune suka Samar da "Hausa Bakwai" ko "Hausa 7". Dukda yake, dansa Karbogari wanda kuyangarsa BaGwariya ta Haifa masa, shima tanada ya Bakawai sune suka mulki Kebbi, Zamfara, Gwari, Jukun, Yoruba, Nupe da Yauri wadanda akekira da "Banza Bakwai" ko "Fake 7"[1]

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Aigbokhai, S.O (1971). West African History for the Certificate Year. Great Brittain: George Allen & Unwin Ltd. p. 14. ISBN 0 04 966010 1.