Daurama
Appearance
| Rayuwa | |
|---|---|
| ƙasa | Najeriya |
| Harshen uwa | Hausa |
| Mutuwa | Daura, |
| Ƴan uwa | |
| Abokiyar zama | Bayajidda |
| Yare | Kabara |
| Karatu | |
| Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
| Sana'a | |
| Sana'a |
ruler (en) |

Daurama ko Magajiya Daurama (ƙarni na 9) ta kasance mai mulkin mutanen Hausa wacce ita ce ta kasance Kabara ta ƙarshe a tarihin Daura. Ana ce mata Kabaran Daura. Masu bada labaran gargajiya suna tunata ne a matsayin Sarauniya ne, Uwa ta Daular Hausawa dake Arewacin Najeriya a yankin Nijar (kasa) da kuma Najeriya.[1] Labarin Magajiya Daurama ana bayar da shi ne a labaran jarumtaka na jarumi Bayajidda.

Magajiya Daurama tayi mulki a garin da ake ƙira ko ake cewa Daura.
An saka wa garin sunanta Daura wanda yanzun Daura masarauta ce mai zaman kanta a Jihar Katsina, Najeriya tsohon birni ne a asalin babban birnin masarautar bayan da Daurama ta ɗauke shi daga garin ta mai da shi sabon birnin Daura, wanda aka sama garin sunanta.[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://dbpedia.org/page/Daurama
- ↑ Odiaua, Ishanlosa (2011). "Earth Building Culture in Daura, Nigeria". Terra 2008: Actes de la 10ème Conférence Internationale Sur L'étude Et la Conservation Du Patrimoine Bâti en Terre, Bamako, Mali, 1-5 Février 2008. Getty Publications. p. 120. ISBN 9781606060438.