Sarauniya Daurama
Sarauniya Daurama |
---|
Sarauniya Daurama Yanzu haka akwai babban zanen Macijiya nade da wuƙa a bakin rijiya a bangon ofishin babban sakataren Jihar Katsina, wanda yake nuni ga tarihin Sarauniya Daurama, wanda ya fi shekara dubu.[ana buƙatar hujja]
Sarauniya Daurama ta gaji sauran yan'uwanta mata wajen sarauta domin wancan lokacin mata ne suke sarautar masarautar. Ita ce ta tara (9) a cikin jerin mata da sukayi sarautar daura.[1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]A lokacin Sarauniya Daurama ne Bayajidda ya zo wanda tarihi ya nuna ɗan Sarkin Bagdaz ne wanda yaƙi ya koreshi daga kasarsa. Ya sauka a Daura da daddare inda ya nemi ruwa, sai tsohuwar da ta sauke shi take faɗa masa ba a samun ruwa sai dai ya jira zuwa gobe Juma’a da safe, inda ya bukaci ta kai shi wajen rijiyar domin ganin abin da ke hana su samun ruwan kullum. Ya saka guga ya ɗibi ruwa sai macijiya ta fito shi kuma ya yi amfani da takobinsa ya sare kan macijiyar, hakan ya sanya mutanen Daura ɗibar ruwa kullum.Takobin bayajidda yanzu ya zama alama ta Masarautar Daura inda duk wanda ya yi sarauta a Daura sai an bashi takobi.[1]
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.