Jump to content

Nijar (ƙasa)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Nijar (kasa))
Nijar
Tutar Nijar Tambarin Nijar
Tutar Nijar Tambarin Nijar


Take L'Honneur de la Patrie (mul) Fassara (22 ga Yuni, 2023)

Kirari «Fraternité, Travail, Progrès»
«Fraternity, Work, Progress»
«Братство, труд, прогрес»
«Brawdoliaeth, Gwaith, Datblygiad»
Suna saboda Nijar
Wuri
Map
 17°N 10°E / 17°N 10°E / 17; 10

Babban birni Niamey
Yawan mutane
Faɗi 21,477,348 (2017)
 Yawan mutane 16.95 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Hausa
Labarin ƙasa
Yawan fili 1,267,000 km²
Wuri mafi tsayi Mont Idoukal-n-Taghès (2,022 m)
Wuri mafi ƙasa Nijar (200 m)
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Faransanci Yammacin Afirka
Ƙirƙira 1960
Ranakun huta
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Cabinet of Niger (en) Fassara
Gangar majalisa National Assembly (en) Fassara
 shugaban Jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tchiani (28 ga Yuli, 2023)
 Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine (8 ga Augusta, 2023)
Ikonomi
Nominal GDP (en) Fassara 14,915,002,098 $ (2021)
Kuɗi CFA franc Yammacin Afirka
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Suna ta yanar gizo .ne (mul) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +227
Lambar taimakon gaggawa 17 (mul) Fassara da 18 (en) Fassara
Lambar ƙasa NE
Niger, Niamey, Place du Liptako-Gourma
Tutan nijar

Nijar ko Nijer[1][2] ƙasa ce da ke yankin Afrika ta Yamma. Tana maƙwabtaka da ƙasashe bakwai (Najeriya daga kudu, Libya daga arewa maso gabas, Aljeriya daga arewa maso yamma, Mali daga yamma, Burkina faso da Benin daga kudu maso yamma, Chadi daga gabas). Tana da al'umma da ta kai fiye da mutum miliyan sha bakwai (17) Kuma tana da ƙabilu daban-daban, kamar su: Hausawa, Zabarmawa, Abzinawa, Fulani, Kanuri, Bugaje, Barebari, Larabawa, Tubawa, da Gurmawa. Nijar ta na ɗaya daga cikin ƙasashen ƙungiyar tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Africa. (CEDEAO). Nijar tana da faɗin ƙasa kimanin 1,270,000Km (490,000sq mi) ta biyu 2 a fadin ƙasa, a ƙasashen Afirka ta yamma. Wajan 80% na ƙasar saharah ne, wajan 22 million mutanan ƙasar Nijar musulmai ne

Mohammed Bazum Tsohon Shugaban Ƙasar Wanda Sojoji Suka Yi Wa Juyin Mulki

Nijar ta samu 'yancin kanta a shekara ta 1960 daga Turawan mulkin mallaka na kasar Faransa. Tana da arziƙin ma'adanai na cikin ƙasa kamar zinariya, da ƙarfe, da gawayi, da uranium, da kuma fetur.

Al'umman Nijar 2013

[gyara sashe | gyara masomin]

A lissafin kasafin ƙasa da INS ta fitar [3], a shekara ta 2013, ƙasar Nijar tana da al'umma milyan sha bakwai da dubu ɗari da ashirin da tara da saba'in da shida (17,129,076).

Manyan Birane

[gyara sashe | gyara masomin]
Niamey, Babban Birnin Nijar kuma mafi girma
Zinder, ta biyu a girma a Nijar.
Maradi, ta uku a girma
Agadez
wasu daga cikin manyan gine-ginen kasar nijar

Yankunan Gwamnatin kasar Sune kamar haka:

Birane da ke da adadin al'umma samada dubu goma (10,000) akan kidayar shekara ta 2012.

Birni Kidaya Yankin Yawan Mutane
2012[4]
Kasantuwa[5]
Abalak Tillabéri 11,068
AbalakTahoua21,84215.4522222|6.2783333format=dec)
AgadezAgadez110,49716.9738889|7.9908333format=dec)
AguiéMaradi17,39713.5080556|7.7772222format=dec)
ArlitAgadez78,65118.7325|7.3680556format=dec)
Ayourou Tillabéri 11,528
Balléyara Tillabéri 16,063
Birnin GaouréDosso14,43013.0877778|2.9169444format=dec)
Birnin-Konni (birni)Tahoua63,16913.8|5.25format=dec)
Bouza Tahoua 10,368
DakoroMaradi29,29313.8166667|6.4166667format=dec)
DiffaDiffa39,96013.3155556|12.6088889format=dec)
DogondoutchiDosso36,97113.6461111|4.0288889format=dec)
DossoDosso58,67113°02′40″N 3°11′41″E / 13.0444444°N 3.1947222°E / 13.0444444; 3.1947222
FilinguéTillabéri12,22414°21′00″N 3°19′00″E / 14.35°N 3.3166667°E / 14.35; 3.3166667
GayaDosso45,46511°53′16″N 3°26′48″E / 11.8877778°N 3.4466667°E / 11.8877778; 3.4466667
Gazaoua Maradi 14,674
GouréZinder18,28913°59′13″N 10°16′12″E / 13.9869444°N 10.27°E / 13.9869444; 10.27
Gidan-RumjiMaradi17,52513°51′00″N 6°58′00″E / 13.85°N 6.9666667°E / 13.85; 6.9666667
IllélaTahoua22,49114°27′42″N 5°14′51″E / 14.4616667°N 5.2475°E / 14.4616667; 5.2475
Kéita Tahoua 10,361
KolloTillabéri14,74613°18′31″N 2°19′51″E / 13.3086111°N 2.3308333°E / 13.3086111; 2.3308333
MadaouaTahoua27,97214°06′00″N 6°26′00″E / 14.1°N 6.4333333°E / 14.1; 6.4333333
Madarounfa Maradi 12,220
MagariaZinder25,92814°34′00″N 8°44′00″E / 14.5666667°N 8.7333333°E / 14.5666667; 8.7333333
Maïné-SoroaDiffa13,13613°13′04″N 12°01′36″E / 13.2177778°N 12.0266667°E / 13.2177778; 12.0266667
MaradiMaradi267,24913°29′30″N 7°05′47″E / 13.4916667°N 7.0963889°E / 13.4916667; 7.0963889
MatameyeZinder27,61513°25′26″N 8°28′40″E / 13.4238889°N 8.4777778°E / 13.4238889; 8.4777778
Mayahi Maradi 13,157
MirriahZinder28,40713°42′51″N 9°09′02″E / 13.7141667°N 9.1505556°E / 13.7141667; 9.1505556
NguigmiDiffa23,67014°15′10″N 13°06′39″E / 14.2527778°N 13.1108333°E / 14.2527778; 13.1108333
NiameyNiamey Capital District978,02913°31′00″N 2°07′00″E / 13.5166667°N 2.1166667°E / 13.5166667; 2.1166667
Wallam Tillabéri 10,594
SayTillabéri13,54613°06′29″N 2°21′35″E / 13.1080556°N 2.3597222°E / 13.1080556; 2.3597222
TahouaTahoua117,82614°53′25″N 5°16′04″E / 14.8902778°N 5.2677778°E / 14.8902778; 5.2677778
TânoutZinder20,33914°58′13″N 8°53′30″E / 14.9702778°N 8.8916667°E / 14.9702778; 8.8916667
TchintabaradenTahoua15,298
TéraTillabéri29,11914°00′38″N 0°45′11″E / 14.0105556°N 0.7530556°E / 14.0105556; 0.7530556
TessaouaMaradi43,40913°45′12″N 7°59′11″E / 13.7533333°N 7.9863889°E / 13.7533333; 7.9863889
Tibiri Maradi 25,513
TillabériTillabéri22,77414°12′22″N 1°27′12″E / 14.206146°N 1.453457°E / 14.206146; 1.453457
Torodi Tillabéri 11,813
ZinderZinder235,60513°48′00″N 8°59′00″E / 13.8°N 8.9833333°E / 13.8; 8.9833333

Masana da masu ruwa a tsaki da gwamnatin mulkin soji ta Jamhuriyar Nijar ta tara domin tsara makomar ƙasar sun kammala taron ƙasa da suka kwashe kwana biyar suna gudanarwa.[6]

Taron ya fara ne daga ranar Asabar 15 ga watan Fabarairu, zuwa Alhamis 20 ga watan na Fabarairu.[7]

Shugaban mulkin soji na ƙasar Abdourahamane Tchiani ne ya kira taron domin seta hanyar da ƙasar za ta bi a shekaru masu zuwa.[8]

Tun farko, bayan juyin mulkin da sojojin suka yi wa Mohammed Bazoum, gwamnatin sojin ta Nijar ta nuna alamun cewa za ta iya mayar da mulki ga farar hula cikin shekara uku, sai dai sakamakon taron ƙasar ya nuna akasin haka.[9]

Ga wasu daga cikin abubuwan da taron ya cimma:

Tabbatar da Tchina a matsayin shugaban ƙasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Taron haɗin kan ƙasar na Jamhuriyar Nijar ya amince da sauya yadda ake kiran jagoran juyin mulkin ƙasar zuwa 'shugaban ƙasa'.[10]

Taron ya ce ya cimma matsayar ne bayan la'akari da "jagorancin" da Tchiani ya nuna wajen sake ƙwato wa Nijar "ƴancinta".[11]

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta shekara biyar

[gyara sashe | gyara masomin]

Taron ƙasar ta Jamhuriyar Nijar ya amince da samar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta tsawon shekara biyar, wadda ita ce za ta tsara yadda za a mayar da ƙasar kan tafarkin dimokuraɗiyya[12]

A lokacin gabatar da jawabi kan matsayar da taron ya cimma, ɗaya daga cikin jagororin taron, Bibata Niandou ta ce: "Miƙa mulki zai kasance a cikin wata 60, wato shekara biyar, daga ranar da aka amince da wannan tsari."[13]

Sai dai ta ƙara da bayanin cewa wa'adin da aka ɗiba na mayar da mulkin ga farar hula zai iya "sauyawa" bisa la'akari da "yanayin tsaro" a ƙasar.[14]

Taron ya yarda cewa jagororin mulkin sojin ƙasar za su iya tsayawa takara a zaɓen da za a gudanar bayan shekara biyar na riƙon ƙwarya.[15]

Dama wannan na daga cikin manyan abubuwan da aka shirya samun matsaya a kan shi.[16]

Hakan na nufin shugaban mulkin soji na ƙasar a yanzu na da damar tsayawa takara.[17]

Wannan na daga cikin ɗabi'un shugabannin mulkin soji a nahiyar Afirka, inda sojojin da suka yi juyin mulki kan rikiɗe zuwa shugabannin farar hula ta hanyar zaɓe.[18]

Na baya-bayan nan shi ne zaɓen da aka yi wa Mahamat Idris Deby a matsayin shugaban ƙasa bayan kasancewarsa shugaban ƙasar soji sanadiyyar mutuwar mahaifinsa.[19]

Ƙara wa Tchiani muƙami

[gyara sashe | gyara masomin]

Ɗaya daga cikin mataimakan shugaban taron, Abdoulaye Seydou ya kuma bayyana cewa taron ya amince da ƙara wa shugaban mulkin soji na ƙasar Abdourahamane Tchiani daga Birgediya-Janar zuwa Janar na soja.[20]

  • Me ake tsammani daga babban taron ƙasa na Jamhuriyar Nijar?
  • Ƙasashen da cin hanci da rashawa suka yi wa katutu a 2024 - Rahoto
  • Me zai faru bayan ficewar ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas?

A yanzu dai za a gabatar wa majalisar mulkin sojin Jamhuriyar Nijar matsayra da taron ya cimma domin amincewa tare da ɗaukar matsaya ta ƙarshe.[21]

Taron ya ƙunshi mutane kimanin 700, waɗanda suka fito daga ɓangarori da dama na ƙasar, da suka haɗa da tsofaffin ministoci da masana da lauyoyi da sojoji da malamai da kuma ƴan ƙungiyoyi masu zaman kansu.[22]

Jamhuriyar Nijar na daga cikin ƙasashe uku - Burkina Faso, Mali da Nijar - waɗanda suka tsame kansu daga ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka, tun bayan juyin mulkin soji da suka faru a ƙasashen.[23]

Haka nan sun raba-gari da ƙasashen yammacin duniya, ciki har da uwar-gijiyarsu, Faransa, sannan suka karkata alaƙarsu zuwa Rasha.[24]


Ƙasashen Afirka
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe
  1. "ISO 3166". ISO Online Browsing Platform. Archived from the original on 17 June 2016. Retrieved 12 May 2017.
  2. "UNGEGN World Geographical Names". United Nations Statisticsc Division. 1 March 2017. Archived from the original on 28 July 2011. Retrieved 12 May 2017.
  3. (http://www.stat-niger.org/statistique/)
  4. Population figures from citypopulation.de, citing (2001) Institut National de la Statistique du Niger.
  5. fallingrain.com.
  6. Bbc
  7. Bbc
  8. Bbc
  9. bbc
  10. Bbc
  11. Bbc
  12. bbc
  13. Bbc
  14. Bbc
  15. Bbc
  16. bbc
  17. bbc
  18. bbc
  19. bbc
  20. bbc
  21. Bbc
  22. Bbc
  23. bbc
  24. Bbc