Dogondoutchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Dogondoutchi
Niger, Dogondoutchi (1).jpg
municipality of Niger
ƙasaNijar Gyara
babban birninDogondoutchi Department Gyara
located in the administrative territorial entityDogondoutchi Department Gyara
located in or next to body of waterDallol Maouri Gyara
coordinate location13°39′0″N 4°2′0″E Gyara
located in time zoneUTC+01:00 Gyara
twinned administrative bodyOrsay Gyara

Dogondoutchi ko (Dogon Dutse a Hausa ta mutanen Najeriya) birni ne dake kilomita 300 daga gabashin birnin Niamey na kasar Nijer, kuma kilomita 40 daga iyakar Nijar da Najeriya. Birnin na kan babbar hanyar da ta hada baban birnin kasar da Maradi da Zinder har zuwa gabashi da Arewacin yankunan Tahua, Agadez da Arlit. Dogondoutchi cibiyar gudanarwa ta yankun rayawa na Dogondoutchi a Jamhuriyar Nijar. Yana karkashin jahar Dosso kuma. Al'umar yankin zaikai kimanin 80,000.

Yanayin muhalli[gyara sashe | Gyara masomin]

Yankin Dogondoutchi[gyara sashe | Gyara masomin]

Daga Arewacin garin Dogondoutchi akwai manyan tsaunuka wanda daganan ne ma garin ya samo asalin sunan sa. Sannan kuma garina yana gefen kogi ne. Sannan garin yana a Kudu maso gabashin Nijar ne tsakanin Sahel da kudu yankin da ake samu wadataccen ruwan sama.

Akwai yanayin samun isasshen ruwan sama a yankin .

Geographic map of Dogondoutchi

Ruwan sama da Zaizayar kasa[gyara sashe | Gyara masomin]

Yawan mutane[gyara sashe | Gyara masomin]

Mazaunan asali[gyara sashe | Gyara masomin]

Akwai mutane kimanin 80,000 (kidayar 2011) akwai akalla mutane 30,000 a yankin birni. Akwai yankunan rayawa guda 11 da kauyuka 17 da kabilun Fulani 5. Kabilin yankin sun hada da Hausawa da Fulani da Abzinawa da Djerma (zabarmawa). Dogondoutchi shine mahadar yamma ta al'umar Hausawa sosai, wadanda sune kabilu mafiya yawa a yankin.

Addini[gyara sashe | Gyara masomin]

Kaso 90% na mutanen Musulunci ne addinin su, sai kuma masu bin addinin gargajiya kamar Bori na wadansu Hausawa. Sannan kuma akwai adadin masu bin Kirista kalilan a birnin.