Niamey
![]() | ||||
---|---|---|---|---|
Ɲamay (mis) Yamai (ha) ⵏⵉⴰⵎⵢ (mis) | ||||
![]() | ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Jamhuriya | Nijar | |||
Babban birnin | ||||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 1,026,848 (2012) | |||
• Yawan mutane | 4,291.05 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 239,300,000 m² | |||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Nijar | |||
Altitude (en) ![]() | 207 m | |||
Tsarin Siyasa | ||||
• Shugaban gwamnati |
Barry Bibata Niandou (en) ![]() | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | ||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NE-8 |
Niamey babban birnin kasar Nijar ne. Wannan birnin yana a matsayin babbar gundumar Birni kuma ya hada gunduma biyar ne. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2011, jimillar mutane 1,302,910 (miliyan ɗaya da dubu dari uku da biyu da dari tara da goma). An gina birnin Niamey a farkon karni na ashirin bayan haifuwan annabi Issa. Babban kogin nan na "Niger" wanda cibiyarshi take tsakanin Sierra Leone da Guinée, ya ratsa birnin Niamey.
Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]
Birnin Niamey ya fara ci gaba ne wajen shekarar 1900, a daidai wani waje inda Fulanin Koira, Gaweye, Kalley, Maourey, Zongo, Gamkalé da Saga suke a lokacin. Kabilar da tafi yawa sune Zabarmawa ko kuma Songhai. Turawa sun iso Niamey ne a makare saboda tana can yammacin kasar inda babu wani kasuwanci da akeyi. Mutanen Gurmance (Gourmantché) ne suka fara rayuwa a yankin Niamey. Amma, wadanda suka kafa kauyen Niamey, Arawa ne da suka zo daga Matankari.