Kusugu
Kusugu | |
---|---|
General information | |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 13°02′11″N 8°19′04″E / 13.0364°N 8.3178°E |
Kasa | Najeriya |
Territory | Daura |
Rijiyar Kusugu tsohuwar rijiya ce wacce take a garin Daura Jihar Katsina, Nijeriya. Rijiyar ta shahara saboda nasabarta da labarin jarumi Bayajidda mutumin da ya kashe macijiya. Rijiyar da kuma wuƙar Bayajidda da ake tsammani yanzu ta zama wurin jan hankalin masu yawon buɗe ido.
Labarin
[gyara sashe | gyara masomin]Dangane da tatsuniyoyin Hausa, al'ummomin Hausawa suna zaune a cikin Sudan ta Tsakiya (yawancin Arewacin Nijeriya ta yanzu da wasu yankuna na Nijar) sama da shekaru 2000. Garin Daura yana ɗaya daga cikin manya-manyan garuruwan hausa na wancan lokacin. Tana da sarakuna a matsayin shugaban gwamnati waɗanda ke kula da al'amuran mutane. A zamanin Sarauniya Daurama, babbar hanyar samun ruwa ga Daura itace rijiyar Kusugu. Amma ana barin mutane su ɗebi ruwa ne kawai a ranar Juma'a saboda wata baƙuwar macijiya da ke zaune a cikin rijiyar.
A haka mutane suka kasance suna ɗibar ruwa a iya ranakun juma'a kawai har zuwa lokacin da wani mutum yazo wanda aka haƙiƙance ɗan sarkin Bagadaza ne. Bayajidda (Abu Yazid) ya zo Daura gama ba ya iya samun kursiyin bayan mutuwar mahaifinsa. Jarumin Yarima bayan ya sauka a gidan wata tsohuwa da sunan Ayyana, ya nemi a ba shi ruwa, amma ba a ba shi abin da ya ishe shi ba. Sannan ya nemi a nuna masa rijiyar domin diban ruwa. An yi masa gargaɗi game da baƙon maciji. Ya tafi bakin rijiyar kuma daga karshe ya kashe macijin bayan fada. Sarauniya ta aure shi kuma ya zama Sarki. Saboda baya iya magana da hausa a da, sai mutane suka fara kiransa da Bayajidda, ma'ana, baya fahimta a da.
Yana da 'ya'ya bakwai waɗanda suka mulki a kasar Hausa guda bakwai wadanda ake kira Hausa Bakwai. Rijiyar Kusugu itace inda aka kashe katon macijin Sarki tare da wani wanda Bayajida yayi a karni na 10 saboda macijin zai baiwa mutanen Daura damar debo ruwa kawai daga rijiyar sau daya kawai a mako, galibi Juma'a.
Isowar Bayajidda a garin Daura da yankan maciji
[gyara sashe | gyara masomin]Bayajidda ya bar matarsa da 'yarsa a Garun Gabas kuma ya ci gaba zuwa ƙauyen Gaya da ke kusa da Kano - wanda wasu ke ganin Gaya ce a Nijar ta zamani -, inda ya sa maƙerin wurin suka sanya shi wuƙa. Daga nan ya zo garin Daura (wanda ke cikin jihar Katsina ta yanzu ), inda ya shiga wani gida ya nemi wata tsohuwa ruwa. [1]Ta sanar dashi cewa maciji mai suna Sarki ( sarki shine kalmar hausa a turance ) yana tsare rijiyar kuma ana barin mutane su debi ruwa sau daya kawai a sati. Bayajidda ya nufi rijiyar ya kashe macijin da takobi ya sare kansa da wuƙar da maƙerarin suka yi masa, bayan ya sha ruwan, ya sa kansa a cikin jaka, ya koma gidan tsohuwar. (Rijiyar da aka ce wannan ya faru a zamanin yau yawon shakatawa ne.)[2][3]
Washegari, mutanen Daura suka taru a bakin rijiyar, suna mamakin wanda ya kashe macijin; Magajiya Daurama, sarauniyar yankin ta ba da ikon mallakar rabin garin ga duk wanda zai tabbatar da cewa ya kashe macijin. Maza da yawa sun kawo kawunan maciji a gaba, amma kawunan bai dace da jikin ba. Tsohuwar, mai gidan Bayajidda da ke zaune ta sanar da sarauniyar cewa bakonta ya kashe shi, bayan haka kuma Daurama ya kirawo Bayajidda. Bayan ya gabatar da kan macijin, ya tabbatar mata da cewa shi ne ya kashe Sarki, sai ya yi watsi da tayin rabin garin maimakon ya nemi aurenta; ta aure shi ne saboda godiyar kashe macijin.[4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Hausa". University of Iowa. Archived from the original on 6 January 2007. Retrieved 2006-12-20.
- ↑ Dierk Lange. "Oral version of the Bayajida legend" (PDF). Ancient Kingdoms of West Africa. Retrieved 2006-12-21.
- ↑ "Katsina State". ngex.com. NGEX, LLC. Archived from the original on 17 February 2007. Retrieved 2007-01-20.
- ↑ Hallam, W. K. R. (1966). "The Bayajida Legend in Hausa Folklore". The Journal of African History. 7 (1): 47–60. doi:10.1017/s002185370000606x. ISSN 0021-8537.