Ajami

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Ajami
Type
Parent systems
  • Ajami

Ajami tsarin rubutu ne na Hausa ta hanyar amfani da haruffan Larabci. Wannan rubutun ya samo asali daga lokacin da addinin Musulunci ya shigo kasar Hausa a karni na shida Miladiyya. Sai dai kuma, kasancewar kwayoyin sautin larabci sun bambanta da na Hausa musamman tagwayen bakake irin su "gy" da "ts", sai kowanne marubuci ya zamo ya na amfani da ta sa dabarar wurin rubutun ajami. Sakamakon haka, ajami ya ke da wuyar ganewa har ma ake ma sa kirari da, gagara-mai-shi.