Jump to content

Maguzawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maguzawa

[1][2]Maguzawa; mutane ne waɗanda asalinsu Hausawa ne masu bautar Gumaka ko Dodanni ko Rana ko Ɗan-maraki ko tsinburbura da dai sauransu. Amma duk da cewa al'ummar Hausawa sun kasance a kan wannan al'ada ta bautar dodanni, sai dai bayan zuwan Addinin Musulunci ƙasashen Hausawa sai suka bar dukkanin waɗancan al'adun kuma sukai watsi dasu.

Hausawa sun rungumi sabon addinin da suka samu sa'annan suka watsar da duk al'adarsu wadda bata dace da Addinin Musulunci ba, amma sai dai an sami wasu daga cikin Hausawan waɗanda basu koma zuwa Musulunci ba tun a waccan lokacin, to sune Hausawan da Musulunci ke kira da Maguzawa, ana kiran namijin da "Bamaguje", mace kuma "Bamagujiya", sannan al'ada da suka ci gaba dabi ta Hausawa, ana kiranta da "Maguzanci".

[3][4]Har wayau, ana samun Maguzawa a ko'ina a ƙasashen Hausa sai dai basu cika zama cikin mutane ba, wannan ko ya faru ne saboda irin tsangwama da ake yi musu tun a waccan lokacin da suka ƙi su koma Addinin Musulunci, yaƙarsu da Hausawa Musulmi ke yi, shi ya sa suke zama a bayan gari. Sun dogara ne a kan yin noma da Kiwo, mafiya yawan Maguzawa ba su da ilimin zamani, domin dodanninsu ba za su yarda su nemi wani ilimi ba. Su dai Maguzawa mutane ne Hausawa da yawancinsu manoma ne, kuma suke a ƙauyukan ƙasar Hausa.

Malam Ibrahim ya ce mutane ne masu ƙwazo da ƙoƙari, sai dai yawancinsu ba Addinin Musulunci suke bi ba, kamar wadanda suke tare da su a yankunan da suke, amma daga baya sannu a hankali wasu daga cikinsu na shiga Musulunci.

Ya ƙara da cewa al'adunsu da yarensu, da kuma sutura sun dace da Hausawa musamman kafin Jihadin Shehu Ɗanfodio. Hausawa musamman a lokacin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo suna nan birjik a wurare da dama musamman kamar wasu ƙauyuka a ƙasar Kano da ma Katsina. Abin da aka fi karkata a kai na tarihi a cewar masanin shi ne mutane ne wadanda suka zo daga Habasha tun ana kiransu Majusu, suka riƙa sauya suna har aka dawo ana kiransu da Maguzawa.

Da yawan masu tarihi na ganin cewa su ne asalin Hausawa, daga baya suka ilimantu suka zama Hausawan da aka sani a yanzu. To amma ya ce daga baya an samu ƙaulani, domin wasu na ganin cewa alama ta fi nuna cewa mutanen Afrika ta arewa ne, domin al'adar da ta fito daga nan irin tasu ce, kafin su dawo arewacin Afrika. Akwai mutanen da suka zo daga Habasha suka zauna a Dutsen Dala da ke Kano, kuma mashahurin sarkinsu shi ne Barbushe, wadannan mutane sun rika bautar gumaka, su kuwa Maguzawa da aka sani a yanzu ba sa bautar gumaka, amma suna da nasu abubuwan na tsaface-tsaface.


https://bbchausa.com