Bagauda

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Bagauda
Rayuwa
Sana'a
Sana'a sarki

Bagauda, wanda aka fi sani da Daud Bagauda ko Yakano, shi ne Sarkin Kano na farko, wanda ya yi sarauta daga shekara ta 998 zuwa shekara ta 1063. Ya kafa Daular da za ta ci gaba da mulkin jihar sama da shekaru 800. A cewar Tarihin Kano, duk Sarakuna da Sarakunan Kano da suka biyo baya sun fito daga zuriyar sa.[1] Ya Kafa daula wadda tayi mulki sama da shekaru 800. A tarihi na Kano dukkan sarakuna da Sultan na Kano daga tsatson shi suka fito.[2]

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

Baban Bagauda shine Bawo ( kuma ana faɗa Bauwo). Bagauda nada ɗa Warisi (sarki), da Saju. Warisi sya gaki mahaifinsa sarki a shekara ta 1063.

Waƙar Bagauda[gyara sashe | gyara masomin]

Waƙar Bagauda waƙa ce ta gargajiya ta Hausa da aka rubuta don girmama Bagauda. [3] [4]

Tarihin Kano[gyara sashe | gyara masomin]

Tarihi ne na Bagauda daga wani Bature mai suna Palmer a shekara ta 1908 Fassarar turanci na tarihin Kano.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Hiskett, M. (1957). "The Kano Chronicle". Journal of the Royal Asiatic Society of Great Britain and Ireland (1/2): 79–81. ISSN 0035-869X. JSTOR 25201990.
  2. Palmer, H. R. (1908). "The Kano Chronicle". The Journal of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland. 38: 58–98. doi:10.2307/2843130. ISSN 0307-3114. JSTOR 2843130.
  3. Hiskett, M. (1965). The 'Song of Bagauda': A Hausa King List and Homily in Verse (II). Bulletin of the School of Oriental and African Studies, University of London, 28(1), 112-135.
  4. Hiskett, M. (1965). The 'Song of Bagauda': A Hausa King List and Homily in Verse (III). Bulletin of the School of Oriental and African Studies, University of London, 28(2), 363-385.