Tambarin Najeriya
Tambarin Najeriya | |
---|---|
national coat of arms (en) | |
Bayanai | |
Farawa | 20 Mayu 1960 |
Applies to jurisdiction (en) | Najeriya |
Depicts (en) | Costus spectabilis (en) , doki, Nijar, Benue da eagle (en) |
Tambarin Najeriya ko Kan Sarki wata alama ce gwamnatin Najeriya take amfani da ita a hukimance a matsayin hatin kasa. Tambarin na dauke da hotuna kamar haka; Akwai Mikiya daga sama, tana nuni da karfin Najeriya, sai fararen dokuna biyu a gefe da gefe, suna nuna martabar Najeriya, akwai kuma zane biyu daya daga hagu dayan daga dama sun hade a waje guda, suna nuna kogunan Neja da na Benue da mahadar su a Lokoja. Wannan bakin da zane yabi ta kansa kuma yana nuna albarkatun kasar da Najeriya ke dashi ne. Koriyar ciyawa ta kasa kuma na nuna arzikin Najeria.[1]
Jar fulawa ta ciki na nuna fulawar Najeriya Costus spectabilis, anzabi wannan fulawar ne saboda ana samun ta a ko'ina a sassan Najeriya.
Alamomim gwamnati
[gyara sashe | gyara masomin]-
Tambarin shugaban kasa
-
Tambarin mataumakin shugaban kasa
-
Tambarin Yan majalisu
-
Tambarin Sanatoci
Alamomin Jahohi
[gyara sashe | gyara masomin]Wasu jahohin nada nasu tambarin.
-
Edo
-
Bauchi
Alamomi na tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Wasu tambari wadanda akayi amfani dasu a baya.
-
Tambarin yankin Mulkin mallaka na Ingila a yammacin Afrika
-
Tambarin Mulkin mallaka na Lagos
-
Tambarin Mulkin mallaka na man Rivers
-
Tambarin mulkin mallaka na Niger Coast
-
Tambarin Mulkin mallaka na Arewacin Najeriya
-
Tambarin Mulkin mallaka na kudancin Najeriya
-
Tambarin mulkin mallakar Najeriya.
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "National Symbols - Emblem". Nigeria's 50th Independence: Celebrating Greatness. Archived from the original on May 6, 2011. Retrieved May 21, 2012.