Tutar Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Wikidata.svgTutar Najeriya
national flag (en) Fassara
Flag of Nigeria.svg
Bayanai
Farawa 1 Oktoba 1960
Applies to jurisdiction (en) Fassara Najeriya
Nau'in vertical triband (en) Fassara
Aspect ratio (W:H) (en) Fassara 2.00:1 (en) Fassara
Color (en) Fassara green (en) Fassara da white (en) Fassara
Depicts (en) Fassara field (en) Fassara da pale (en) Fassara
Tutar Najeriya

Tutar Najeriya an tsarata a shekarar 1959 kuma an gabatar da ita a hukumance a ranar 1 Oktoba, 1960. Tutar na da bamgarori uku wato kore, fari, kore. Korayen guda biyu na nuna arzikin Najeriya yayin da farin na tsakiya ke nuna zaman lafiyar kasar.

Tsarawa[gyara sashe | gyara masomin]

Michael Taiwo Akinkunmi ne ya tsara tutar Najeria a wata gasa da aka shirya ga masu zane na su tsara tutar da zata zama ta Najeriya a 1959. A lokacin Akinkunmi nada shekaru 23 kuma yana dalibi. Yana karatu a makarantar Norwich Technical College a London kasar Ingila, sai yaga sanarwa a jarida ta anaso a zana sabuwar tutar Najeriya. Asalin tutar da Akinwumi ya tsara akwai wata alama a tsakiyar ta, bayan masu tantancewa sun duba ne sai suka cire wannan alamar tare da zabarta. Najeriya dai ta samu yancin kanta ne daga kasar Ingila.[1]

Najeriya nada tutoci daban daban na sassan gudanarwar ta. Wasu jahohin na Najeriya nada nasu tutocin.[2]

Mahadin fitar da kala[gyara sashe | gyara masomin]

Yadda za'a hada tutar Najeriya.

Tsarin Kala Kore Fari
RAL
None
9003
Signal white
CMYK 100.0.39.47 0.0.0.0
Hexadecimals #008753 #FFFFFF
Decimals 0,135,83 255,255,255

Wasu tutocin[gyara sashe | gyara masomin]

Tutocin Jahohi[gyara sashe | gyara masomin]

Tutoci na tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Wadannan sune tutocin Najeriya kafin samun yancin kanta.


Sake duba[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Archived copy". Archived from the original on 2014-07-14. Retrieved 2014-06-30.CS1 maint: archived copy as title (link)
  2. Nigeria: One Nation, Many Flags