Kakuri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kakuri
Bayanai
Ƙasa Najeriya

Kakuri yanki ne a Kadunan Najeriya . Gunduma ce a cikin garin Kaduna kuma tana ƙarƙashin Karamar Hukumar Kaduna ta kudu. Akwai Asibitin St. Gerard da Babban Asibitin Gwamna Awan. [1] [2] Makarantar Sakandare ta Gwamnati, makarantar kula da lafiyar masu tabin hankali da makarantar St. [3] [4] Akwai kuma tashar jirgin ƙasa. [5] Ita ce cibiyar masana'antar Kaduna. Sannan kamfanonin Chemicals-German Chemicals PLC, Prosan Engineering, Peugeot Automobile Nigeria da Chanchangi Motors Ltd. suna aiki a Kakuri. [6] [7] [8] Cocin Christ Apostolic da cocin Anglican na St. Paul suna a Kakuri. [9] duka suna a wajen. Hakanan Kakuri na da makarantar sakandare ta Gwamnati. [10] Matthew Kukah, sannan-Vicar Janar na Cocin Katolika na Kaduna yana zaune a cikin garin Kakuri kuma yanzu bishop na Sakkwato. [11] tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi aiki a rundunar sojoji a Kakuri. Cif Omadachi Egboche tsohon Shugaban Kamfanin bada lasisin Wuta ne na Najeriya (LECAN Kakuri reshe) mazaunin ne. Yankunan da ke kusa da Kakuri sun haɗa da Nassarawa zuwa arewa, dirkania zuwa yamma, Barnawa a gabas da Gonigora zuwa kudu. Kakuri nada kungiyoyi na cigaban al'umma . [12]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. St. Gerard Hospital Kakuri Kaduna. Wikimapia.org. Retrieved on 25 October 2011.
  2. Gwamna Awan General Hospital, Trikania, Kakuri, Kaduna. Wikimapia.org. Retrieved on 25 October 2011.
  3. Bridlington School – using TALMOS Gateway: Nigeria – Dreams and Teams. Bridlingtonschool.eril.net (7 May 2010). Retrieved on 25 October 2011.
  4. Facebook. Facebook.com. Retrieved on 25 October 2011.
  5. Kakuri / Kakuri, Nigeria (general), Nigeria, Africa. Travelingluck.com. Retrieved on 25 October 2011.
  6. NGC Healthcare – One of Nigeria's leading Pharmaceutical Manufacturers and Distributors. Ngcplc.com. Retrieved on 25 October 2011.
  7. Prosan Engineering Company Limited. Prosaneng.com. Retrieved on 25 October 2011.
  8. African Road Transport Network: Kaduna. LogisticsWorld. Retrieved on 25 October 2011.
  9. Conquering Your Giants Archived 2010-11-24 at the Wayback Machine. I-proclaimbookstore.com. Retrieved on 25 October 2011.
  10. JAMES BONIFACE – OnlineNigeria.com Schoolmate. Onlinenigeria.com. Retrieved on 25 October 2011.
  11. Nigeria Is A Superpower In Africa – Says British Broadcaster – Abuja City, Nigeria – Cyblug Archived 2018-09-29 at the Wayback Machine. Abujacity.com (25 June 2010). Retrieved on 25 October 2011.
  12. World Environment Day 5 June 2008 Archived 25 Satumba 2010 at the Wayback Machine. UNEP. Retrieved on 25 October 2011.