Lawal Kaita
![]() | |||
---|---|---|---|
Oktoba 1983 - Disamba 1983 ← Abba Musa Rimi (en) ![]() ![]() | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Katsina, 4 Oktoba 1932 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | Abuja, 2 ga Janairu, 2018 | ||
Yanayin mutuwa |
(liver failure (en) ![]() | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Barewa College (en) ![]() London School of Economics and Political Science (en) ![]() | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Lawal Kaita (An haife shi ne a 4 ga Watan Oktoba 1932 - 2 ga Janairun 2018). ya kasan ce dan siyasan Najeriya ne da aka zaba a jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN) a matsayin gwamnan jihar Kaduna, Najeriya, yana rike da mukami tsakanin Oktoba zuwa Disamba 1983, lokacin da Jamhuriya ta biyu ta Najeriya ta kare da juyin mulkin da ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki.
Rayuwa[gyara sashe | Gyara masomin]
An haifi Kaita a ranar 4 ga Oktoba 1932 a Katsina, a can arewacin arewacin Najeriya. Shi dan uwan Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ne na jini kuma dan gidan sarautar Nagogo, sarakunan gargajiya na masarautar Katsina. Ya halarci Kwalejin Barewa, Zariya (1946 - 19550) sannan daga baya ya yi karatu a Makarantar Tattalin Arziki ta London (1971–1972).. Bayan dawowarsa Najeriya, Kaita ya zama ma'aikacin gwamnatin jihar Kaduna. Ya yi aiki a matsayin Sakatare a Hukumar Ruwa ta Jiha (1973–1975), Kwamishinan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki (1975 - 1977) da Mataimakin Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka na Jihar Kaduna (1976–1977)
Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]
https://guardian.ng/news/kaduna-ex-gov-lawal-kaita-dies-at-85/
https://www.pmnewsnigeria.com/2018/01/02/lawal-kaita-ex-governor-defunct-kaduna-state-dead/