Jump to content

Lawal Jafaru Isa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lawal Jafaru Isa
gwamnan, jihar Kaduna

9 Disamba 1993 - 22 ga Augusta, 1996
Mohammed Dabo Lere - Hamid Ali
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar

Lawal Jafaru Isa, Soja ne Mai ritaya, Birgediya Janar na sojojin Najeriya, kuma ya zama shugaban mulkin soja na jihar Kaduna a watan Disambaa na shekarar 1993 zuwa watan Agusta shekarata 1996 a lokacin mulkin Janar Sani Abacha . A shekarar alit 1996, ya kirkiro masarautu da dama ga mutanen kudancin Zariya ko Kaduna domin a samu zaman lafiya a jihar Kaduna.

A watan Satumbar shekara ta 2000, ya kasance jigo a sabuwar kungiyar tuntuba ta Arewa, wata kungiya mai fafutukar neman siyasa ta yankin arewa. Ya zama shugaban "United Nigerian Development Forum" kungiyar da ke da alaka da yakin neman sake zaben Janar Ibrahim Babangida a takarar shugaban kasa a watan Afrilun shekara ta 2003. Ya kuma zama darakta na bankin PHB.

Ifeanyi Nwolisa yayi rubutu game da shi: “A gaskiya zai wuya na iya tunawa da dukkan gwamnonin jihar Kaduna da suka wuce, amma akwai wanda na fi so wato Laftanar Kanal. Lawal Jafaru Isa wanda ya mulki jihar Kaduna daga watan Disamba shekara ta 1993 zuwa watan Satumba 1996. A lokacin mulkin sa ne Kaduna ta fi samun rashin tsaro domin lokacin akayi rikicin Zongon Kataf wato 1992. Saurin da ya yi da kyakkyawar fahimtar shugabanci sun tabbatar da cewa rikicin bai ta’azzara ba”.

Nwolisa ya kara da cewa, “Na tuna wata haduwa da Laftanar Kanar, a lokacin ina a birged na yara a lokacin tare da mabiya darikar Anglican, a daya daga cikin tarukan da aka shirya a cocin St Michael’s Anglican Church. Lt Col. Lawal Jafaru Isa, duk da cewa musulmi bai da matsala da wajen halartar taro. Hakan yana da kyau domin matakin ya tabbatar da cewa Kiristoci sun soma amincewa da shi kuma sun amince sosai da gwamnatinsa don ta kāre rayukan ’yan ƙasa ba tare da la’akari da addini ba. Kyakkyawar niyyar da Lt Col. Lawal Jafaru Isa yake da ita wajen hada kan daukacin mazauna jihar Kaduna ya samar da abin koyi ga gwamnonin da suka biyo baya, wato yin gaggawar daukar mataki a duk wani abu da ya faru ko da ‘yar karamar matsala ce.”

Rikicin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Isa, babban mai goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ne, ya tsaya takarar gwamnan jiharsa ta Kano sau biyu, tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a Najeriya a shekara ta 1999. Da farko dai ya tsaya takara ne a karkashin sabuwar jam’iyyar CPC ta Buhari a shekarar 2011

Zaben da ya shiga karo na biyu a kan karagar mulki a karkashin jam’iyyar APC shine a shekara ta 2015 bai ga hasken rana ba, bayan da gwamnan jihar na yanzu, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kada shi a zaben fidda gwani na yan takarar jam’iyyar.

Zarge-zargen cin hanci da rashawa

[gyara sashe | gyara masomin]

A lokuta biyu mabanbanta Isa ya tsaya takarar gwamna, ya shirya yakin neman zabensa akan gaskiya. Da yawa daga cikin abokan takararsa da suka hada da Yakubu Ya'u Isa sun yi ikirarin cewa shi tsaftatacce ne kamar Muhammadu Buhari wanda wasu 'yan Najeriya ke yiwa lakabi da mai gaskiya.

Sai dai a ranar 6 ga watan Janairu, na shekarar 2015, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati wato (EFCC), ta kama shi a gidansa da ke Abuja, dangane da binciken da ake yi na yadda aka karkatar da makudan kudade daga ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Isa ya kasance jigo na farko a jam'iyyar APC da (EFCC) ta kama tun bayan fara bincike kan zargin karkatar da dala biliyan 2.1 da aka ware don sayen makamai da jami'an tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ta yi.

An yi amannar cewa Isa babban aminin tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ne wato Col. Sambo Dasuki (Rtrd).

An ce misalin karfe 9 na dare ne jami’an hukumar (EFCC) suka mamaye gidansa, sannan suka tafi da shi bayan ‘yan mintoci. Mako guda kafin a kama Birgediya-Janar, an aike masa da takardar gayyata da ya bayyana a gaban hukumar, a ranar 6 ga watan Janairu don sharewa daga “wasu tambayoyi akan rasidai” daga tsohon NSA. Masu bincike sun yi imanin ya karbi sama da Naira miliyan 100 daga hannun Col. Dasuki.

An gano cewa maimakon girmama gayyatar, majiyoyin sun ce, Janar. Isa ya rubutawa hukumar (EFCC) wasika ta hannun lauyansa, yana neman a dage ranar bayyanarsa bisa dalilin mutuwar dan uwansa. Da alama dai hukumar ba ta gamsu da uzurin nasa ba, sai dai (EFCC) ta kama shi domin ya fayyace "rasidun da ake tambaya a kai".

A baya ma dai an kama shugaban kamfanin <i>Daar Communications</i> Plc, wato Cif Raymond Dokpesi akan kudi naira biliyan 2.1 da aka gano a asusun sa na banki. Ya ce kudaden da ya karba daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a lokacin mulkin Goodluck Jonathan na biyan kudin yakin neman zabe da kuma yakin neman zabe na 2015 ne.

Shima haka Alhaji Attahiru Bafarawa tsohon gwamnan Sokoto yana fuskantar bincike akan kudi har naira miliyan 100 da ya ce ya karba ne domin addu'o'in neman samun nasarar jam'iyyar PDP a zaben shekara ta 2015 mai zuwa. Hakanan ma an kama tsohon ministan kudi, Bashir Yuguda bisa zargin karbar naira biliyan 1.5 daga ofishin tsohon NSA ta hannun wani kamfani da ba a bayyana sunansa ba, kan wani dalili da shima ba a bayyana ba.

Ba da dadewa ba, kakakin jam’iyyar PDP, Cif Olisa Metuh, shi ma an gayyace shi hukumar (EFCC) domin ya amsa tambayoyi akan wasu makudan kudade a asusun wani kamfani da yake da hannayen 0jari masu yawa. Wani ma’aikacin hukumar (EFCC) da ya tabbatar da wani kamfani mai suna Destra Investment Limited wanda Metuh ke da hannun jari a cikinsa, ya karbi kudi har naira biliyan 1.4 daga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Sauran wadanda ake tsare da su sun hada da dan Bafarawa, Sagir Bafarawa, da na tsohon ministan tsaro, Bello Mohammed, Abba Mohammed.

Jerin sunayen ‘yan Najeriya da hukumar (EFCC) ta gayyato na karuwa a duk rana. Da alama ƙarshen binciken ba nan kusa yake ba. Jafaru Isa, jigon APC na farko, ya zama babban kifi a jikkar (EFCC).

Samfuri:KadunaStateGovernors