Musulunci a Najeriya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Mutane sama da 85,000,000 yan Najeriya musulmai ne kenan sama da rabin yan kasar wato 50% ne ke bin tafarkin addinin Musulunci . Mafi yawan musulman Najeriya mabiya koyarwar Sunnah ne wato tafarkin koyi da Manzon Allah (Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata agareshi), Duk da haka da akwai mabiya Dariku da Shi'a marasa rinjaye a wadansu daga cikin biranen kasar kamar Zariya, Borno, Neja, Sokoto, Kano da dai sauran su. Duba Shi'a a Najeriya. Mafi yawan musulman Nigeria mazauna ne na bangaren arewacin kasar, sannan akwai adadin mabiyan musulunci a yankin kudu mask gamma na kasar Nigeria. Akwai kadan daga mabiya Ahmadiyya darikar da ta fara a karni na 19 a kasar Indiya. Kungiyar da take bincike akan harkokin addinai ta Duniya wato Pew Forum on religious diversity tace kash 12%.

Na musulman Najeriya mabiya Shi'a ne, yayin da 3% ke bin Ahmadiyya.