Ahmadiyya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmadiyya
Bayanai
Iri ma'aikata
Ƙasa Punjab (Indiya), British Raj (en) Fassara da Indiya
Tarihi
Ƙirƙira 1889
Wanda ya samar
alislam.org
Liwa-e-Ahmadiyya, Tutar Ahmadiyya
Mirza Ghulam Ahmad

Ahmadiyya (Urdu احمدیہ Ahmadiyya) tafiyar imani ce ta addini wadda aka kafa ta a karni na (19), Mirza Ghulam Ahmad ne wanda mabiyan sa suka hakikance kan cewar shine Mahdi ya kafa tafiyar. An kafa tafiyar ne tun kafin Indiya ta rabu zuwa wannan Indiyar ta yanzu wato rabewar ta da Pakistan da Bangladesh.

Ahmad yaso ya sabunta Musulunci, tare da da'awar dawo da ainahin koyarwa ta addinin Musulunci.a shekara ta alif( 1914), tafiyar ta rabe zuwa gida biyu, a sakamakon wanda zai zamo magajin Ahmad kuma har yanzu wadannan bangarorin sunanan. Mirza Ghulam Ahmad yayi da'awar cewa ya cika annabatar Mahdi. Ana yi masa lakani da Mujaddadi na karni na( 14), kuma Yesun da aka alkawarta zuwan sa.[1][2][3][4][5]

Yan Ahmadiyya na daukar kansu a matsayin Musulmai kuma suna da'awar sunayin addinin Musulunci ne wanda Annabi Muhammad ya koyar. Mirza Ghulam Ahmad ya kafa tafiyar ne a shekara ta alif(1889 ), kuma ya saka mata suna Ahmadiyya Muslim Jamaat Fatan sa shine ya dawo da ruhin Musulunci. .

Ainahin tafiyar Ahmadiyya ya tsage zuwa gidaje biyu[6] bayan rasuwar Nooruddin,magajin Ghulam Ahmad na farko.

Wadannan tafiyoyin biyu sune Jama'ar Ahmadiyya da kuma Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore (Ahmadiyya Anjuman Ishaat-i-Islam, AAIIL). Bangarorin nada bambanci ga hanyar koyarwa a tsakanin su.[6][7]

Babban bangare na Jama'ar Ahmadiyya na da rassa a sama da kasashen duniya (190), babbar cibiyarta na a birnin Landan na Ingila. Karamin tsagin kuma da akafi sani da Jama'ar Ahmadiyya na Lahore nada cibiya a Lahore, kuma anfi sanin su a Jamani, Autraliya da Pakistan.

Abinda ke kawo rigima shine fahtar Ahmadiyya dangane da rasuwa da dawowar Annabi Isah da kuma mahangar su ga Jihadi. Hakanan ma Yan Ahmadiyya Nada bambancin fahimta da ayar nan ta Kur'ani( 33:40. ), Wannan aya tana magana akan cewa Annabi Muhammad shine cikamakon Annabawa. Sai dai mabiya Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore basu da taraddadi dangane da wannan batun domin su basu kallon Mirza Ghulam Ahmad matsayin Annabi. A wannan dalilin ne yasa sukafi kusanci da akidar Musulunci.

Yan Ahmadiyya sun fassara Kur'ani da dukkannin manyan harsunan duniya. Kuma suna yada akidun su da da'awar su awa (24), a tashoshin su na talabijin din su wadanda suka hada da, MTA 1,MTA 2, MTA 3 (domin Larabawa masu kallo) kuma kwanannan suka kaddamar da sabuwar tashar MTA Africa. Yan Ahmadiyya na samar da malamai, likituci,masu kare yancin Dan Adam a kasashen da suka cigaba.

Zarge-Zarge[gyara sashe | gyara masomin]

Musulmai mabiya Sunnah na kallon yan Ahmadiyya da masu aikata Bidi'a saboda imanin da sukayi cewa Ahmad Ghulam Annabi ne kuma shine Mahdi kuma Annabi Isah da zai dawo kuma basu yadda da ce Annabi Muhammad ne Annabin karshe ba.[8][9] Dangane da yadda yaso ya Annabtar da kansa kuwa yace shine Annani Isah kuma yadawo ne domin ya karya Gicciye.[10] Mafi rinjayen musulmai basu danganta Yan Ahmadiyya da wannan sunan, sunadai kallon su ne a matsayin wasu masu wani sabon Addini wanda wani ya samar. Ba kamar Musulunci ba wanda shi Annabi Muhammad ne yazo dashi amma bashine ya samar da shiba.[11].

Akida[gyara sashe | gyara masomin]

fassarar Al'kurani na harsuna daban-daban wanda masu fassara na Ahmadiyya suka fassara

Acikin akida da abubuwan da Yan Ahmadiyya sukayi imani dashi akwai shika-shikan Musulunci guda biyar (wato, Shahada, Sallah, Azumi, Zakka, Hajji) kuma suke yinsu, sannan kuma sunyi imani da shika-shikan imani guda shida kamar dai yadda Musulmai Mabiya Sunnah sukayi. Hakanan kuma sun yadda da Al Kur’ani kuma suna kallon Ka'aba matsayin Alkibla lokacin da zasuyi Sallah, kuma suna bin Sunnah da Hadisi.[12][13][14][15][16]

Alkalumma[gyara sashe | gyara masomin]

Yazuwa shekarar 2016,an kiyasta adadin kasashe( 209) ne a duniya inda za'a iya samun yan Ahmadiyya. Babu kasar da Ahmadiyya ke da rinjaye.[17] A wasu kasashen kamar Pakistan an haramta Ahmadiyya gabatar daya.[18] Gabadaya wannan dalilinne yasa yakasance abu mai wahala ga Ahmadiyya ta kafa wasu kungiyoyinta masu zaman Kansu. Sakamakon haka Yan Ahmadiyya na ikirarin sunkai gwamman miliyoyi;[19] bugu da kari wasu majiyoyi masu zaman kansu sun ruwaito cewar akwai kididdigar adadin jama'ar Ahmadiyya sunkai miliyan( 10 zuwa 20),[20] gaba dayan duniya anyi kiyasin yan Ahmadiyya sunkai adadin kaso( 1% ),na al'umar Musulmai.[21] a shekara ta (2001), wata Insakulofidiya mai suna Christian Encyclopedia ta wallafa cewar Tafiyar Ahmadiyya tafi kowacce darika a Musulunci saurin yaduwa.[22] Ta kuma kiyasta cewa kasar da tafi kowacce yawan yan Ahmadiyya itace Pakistan, da kiyasin (4%), na al'umar kasar. Sai kuma Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore mai mabiya( 0.2% ), a kasar ta Pakistan.[23] An kiyasta cewa yan Ahmadiyya ka iya kaiwa (60,000 zuwa miliyan 1 a Indiya).[24].

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

 1. “The Fourteenth-Century's Reformer / Mujaddid”, from the “Call of Islam” Archived 2017-05-18 at the Wayback Machine, by Maulana Muhammad Ali
 2. Claims of Hadhrat Ahmad,Chapter Two
 3. Reflection of all the Prophets
 4. Future of Revelation, Part 7
 5. The Removal of a Misunderstanding
 6. 6.0 6.1 ""The Split in the Ahmadiyya Movement"by Maulana Muhammad Ali". Archived from the original on 2021-04-12. Retrieved 2019-12-19.
 7. ""Refutation of Maulvi Muhammad Ali's Account of Ahmadiyya Dissensions"". Archived from the original on 2007-10-15. Retrieved 2019-12-19.
 8. Jones, Kenneth W. (1976). Arya Dharm: Hindu Consciousness in 19th-century Punjab. University of California Press. p. 148. ISBN 978-0-520-02920-0.
 9. The Illustrated Weekly of India, Volume 102,Issues 1-2.
 10. Fraser, Gordon (2008). Cosmic Anger: Abdus Salam - The First Muslim Nobel Scientist. Oxford University Press. p. 58. ISBN 978-0-19-157866-3.
 11. Jackson, Roy (2010). Mawlana Mawdudi and Political Islam: Authority and the Islamic state. Routledge. p. 50. ISBN 978-1-136-95035-3.
 12. Annemarie Schimmel et al.: Der Islam III. Volksfrömmigkeit, Islamische Kultur, Zeitgenössische Strömungen. Kohlhammer, Stuttgart 1990, S. 418–420
 13. Marzia Balzani.'An ethnographer among the Ahmadis: Learning Islam in the suburbs' in Gabriele Marranci (ed.) Studying Islam in Practice. Routledge, 2014, p.117.
 14. "Islam", Al Islam Online
 15. Andrea Lathan (2008) ‘The Relativity of Categorizing in the Context of the Aḥmadiyya’ Die Welt des Islams, 48 (3/4): 377
 16. Mirza Ghulam Ahmad (2004) The Essence of Islam, Vol. II, p.129—39, Tilford: Islam International
 17. "The Minority's Minority". Archived from the original on 26 June 2015. Retrieved 16 June 2015.
 18. "The 1974 ouster of the 'heretics': What really happened?".
 19. "An Overview". Al Islam. Retrieved 4 March 2014.
 20. See:
 21. A figure of 10 to 20 million represents 0.62% to 1.25% of the worlds Muslim population.
 22. As of 2001 the Ahmadiyya Movement had been the fastest growing sect according to the World Christian Encyclopedia for a number of decades. For this, see earlier editions. The 2001 edition placed the growth rate at 3.25%, which was the highest of all Islamic sects and schools of thought. See:
  • David B. Barrett; George Thomas Kurian; Todd M. Johnson, eds. (15 February 2001). World Christian Encyclopedia. Oxford University Press USA. ISBN 0195079639.
 23. The Lahore Ahmadiyya Movement has unofficially stated its total population to be up to 30,000, of which 5,000 to 10,000 live in Pakistan. On this basis, the Lahore Ahmadiyya Movement represents approximately 0.2% of the total Ahmadiyya population.See:
 24. "Wretched Of The Land".