Insakulofidiya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Wikidata.svgInsakulofidiya
literary genre (en) Fassara da book form (en) Fassara
Vergleich Wikipedia Brockhaus 2011-07 Athen.png
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na reference work (en) Fassara, knowledge organization system (en) Fassara, tertiary source (en) Fassara, serial (en) Fassara da lexicon (en) Fassara
ISOCAT id (en) Fassara 103
Jadawalin jerin littattafai akan tsarin insakulofidiya
majalisar yaran a kasashen turai a insakulofidiya

Insakulofidiya ko a harshen Turanci Encyclopedia ko kuma Encyclopaedia (daga ye kalmomin harshen Girka ἐγκύκλιος παιδεία), wata hadakar bayanai ce a rubuce (mafiyawanci littafi ne) ko kuma a shafukan yanar gizo. Wato dai akan ce Kamus ne amma shi ya kunshi cikakkun bayanai na kalma ko suna kuma a jere harafi bayan harafi.[1][2][3][4]

Asalin Insakulofiya bugaggune a litattafai har zuwa farkon karni na 20 lokacin da aka fara saka wasu a faifayen CD da kuma a yanar gizo. Insakulofidiya ta karni na 21 mafiyawanci tafi a shafukan yanar gizo ne. Babban shafin yanar gizo daya kunshi Insakulofidiya shine shafin Wikipedia musamman ma dai na Turanci wanda yake da sama da makaloli miliyan 5, saidai shima shafin Wikipedia na Hausa shine babban shafin Insakulofidiya na Hausa na yanar gizo. Babban littafi wanda aka wallafa a na Insakulofifiya a duniya shine littafin Britannica, wasu yarurrukan suna da rubutattun litattafai na Insakulofidiya wasu kuma babu.

An wallafa dubban litattafa wadanda suka kunshi cikakkun ilimai a dubban shekaru da suka gabata. Sananne cikin litattafan farko farko akwai Tarihin halittar Allah na Felin Tsoho. Sunan Encyclopedia ya samo asali ne tun a karni na 16 ma'anar sa (cikakken ilimi). Littafin Encyclopédie (da Faransanci) na Denis Diderot shine littafin Insakulofidiya na farko da mutane da dama suka hadu wajen rubuta shi.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. Béjoint, Henri (2000). Modern Lexicography. Oxford University Press. ISBN 0-19-829951-6.
  2. C. Codoner, S. Louis, M. Paulmier-Foucart, D. Hüe, M. Salvat, A. Llinares, L'Encyclopédisme. Actes du Colloque de Caen, A. Becq (dir.), Paris, 1991.
  3. Bergenholtz, H.; Nielsen, S.; Tarp, S., eds. (2009). Lexicography at a Crossroads: Dictionaries and Encyclopedias Today, Lexicographical Tools Tomorrow. Peter Lang. ISBN 978-3-03911-799-4.
  4. Blom, Phillip 2004. Enlightening the World: Encyclopédie, the book that changed the course of history. Palgrave Macmillan. New York.