Wikipedia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Wikipedia kundin bayanai akan ilimomi daban daban Dan Karin ilimin kowa da kowa kyauta

tambarin shafin Wikipedia
Jimmy Wales babban shugaban Wikipedia
Larry Sanger mutum na biyu wada suka kirkiri Wikipedia

Shafin yanar gizo ne wanda ya hada harsunan duniya masu yawa, a shafin kowa na iya kirkira tare da gyara makala kyauta. Shine babban shafi wanda yake samar da makaloli masu karin bayanai a yanar gizo.

An kaddamar da shafin Wikipedia ne ranar 15 ga Janairu na 2001, Jimmy Wales tare da Larry Sanger ne suka hada gwiwa wajen sammar da shafin. A farkon kirkirar shafin an kafa shine da Turanci amma daga baya kuma aka samar da karin Harsuna akai akai. A halin yanzu akwai makaloli guda 5,652,162 a sashen Turanci wanda kuma shine sashen da yafi kowanne wajen tarin makaloli. Ayanzu akwai alkaluman makaloli guda miliyan arba'in a mabanbantan yarurruka 301, sannan shafin ya samu masu ziyara mabanbanta guda miliyan 500 da kuma masu ziyara adadin duka masu ziyara biliyan 18 ko wanne wata tun daga watan Fabrairu na 2014.

A sashen Hausa na wikipedia kuma akwai makalolin da suka kai guda 1754, duk da yake sashen yana da karancin masu bayar da gudunmuwa amma ahankali sashen yana kara bunkasa cikin gaggawa.

|
Wannan kasida guntu ne: yana bukatar a inganta shi, kuna iya gyarashi.