Jimmy Wales
Jimmy Donal Wales ( /ˈdʒɪmi ˈdoʊnəl ˈweɪlz/) ; an haife shi a ranar 7 ga watan Augusta aa shekara ta 1966 a garin Huntsville da ke jihar Alabama Ƙasar Amurika, yana zaune a Landon da ke Ƙasar Ingila. ɗan kasuwan Kasar Tarayyar Amurka ne. Jimmy Wales da Larry Sanger ne suka ƙirƙirar babbar manhajar Wikipedia a shekara ta 2001. Ya yi karatu a Jami'ar Auburn da Jami'ar Jihar Alabama, Tuscaloosa inda ya samu shaidar digiri na biyu a Jami'ar jihar Indiana, Shahararren Dan kasuwan yanar gizo ne, kuma yana da adadin kudi sama da Dala miliyan daya ($1,000,000) a shekara ta 2014. Shi ne shugaban Wikia, Inc. tun daga shekara ta 2004 har zuwa yau, Mazaunin Shugaban Wikimedia Foundation daga shekara ta 2003–2006, Chair emeritus of Wikimedia Foundation daga shekara ta 2006 har zuwa yanzu, shi ya amshi Florence Devouard a matsayin shugaban Wikimedia Foundation, Babban Dan kungiyar wikimedia Foundation Creative Commons ne, kuma yana daga cikin masu bada shawara a Sunlight Foundation da MIT Center for Collective Intelligence, a Guardian Media Group ya daina bada shawara a watan Afrilun shekaran 2017. Matansa sune;: Pamela Green daga shekara ta (1986 zuwa 1993), Christine Rohan (1997–2011), sai Kate Garvey Wanda tun daga shekara ta 2012 har yanzu suna tare. 'Ya'yansa guda 3 ne mata.