Gudunmuwa
Gudunmuwa |
---|
Asalin Harshe Binciken farko dangane da asalin harshe an gudanar da shi ne bisa umarnin Fir’aunan Misra (Egypt) wanda ya yi zamani a qarni 7. Wannan Far’auna ya umarci bawansa da ya keve wasu tagwaye. Kalmar farko da suka fara furtawa ita ce ‘bekos’ wadda take nufin ‘mummuqi’ a harshen Phrygia da ake amfani da shi a yammacin Persia. Wannan sarki ya yi iqirarin cewa, harshe Phrygia shi ne harshen asali wanda ragowar harsunan duniya suka samo asali daga gare shi. Wannan bincike yana da rauni. Har ila yau, sarkin Scotland ya gudanar da makamancin wannan bincike, inda ya ware wata bebiyar mace wanda ya haxa ta da qananan yara domin gano harshen asali. Wannan ya samar musu da duk wani abu na rayuwa wanda ya haxa da abinci, da ruwa, d s. Kalmar farko da suka fara furtawa a yayin da suka kai munzalin Magana ta fito ne daga harshen ‘Hebrew’. Don haka, wannan sarki shi ma ya yi iqirarin cewa, harshen Hebrew shi ne harshen da aka fara Magana da shi.
Ra’o’in Asalin Harshe.
Akwai ra’a’yoyi daban-daban wa’inda suka bayyana asalin harshe. A nan za mu yi qoqarin kawo wasu tare da bayyana rauninsu dangane da da’awarsu game da asalin harshe.
Ra’in Bow-Wow
Wannan ra’in na ganin cewa harshe ya samo asali ne daga kwaikwayon sautukan dabbobi d.s. Masu wannan ra’ayi sun dogara bisa kalmomin amsa-kama.
Raunin Ra’i
1. Kalmomin amsa kama ba su da yawa a cikin harsuna. Hakazalika, kowane harshe yana da irin tasa hanyar da yake bayyana sautukan asali (natural sounds)
2. Har ila yau, wannan ra’i ya yi watsi da daya daga cikin siffofin harshen Dan-Adam – wato rashin alaqa tsakanin sauti da ma’anarsa.
Ra’in Pooh-Pooh Jean Jacquest R. ne ya samar da wannan ra’i a qarni na 18, inda ya yi iqirarin cewa, harshe ya samo asali ne sakamakon zafi ko haushi ko murna (instinctive emotional cries). Jean ya dogara ne bisa sautukan motsin rai kamar ‘ah!’ hey! d.s. wadanda harsunan duniya ke amfani da su.
Rauni Ra’i
1. Rashin yawan sautukan motsin-rai a harsuna. b. Ajiyar zuciya da sauran sautukan motsin rai ba su da alaqa da baqi da wasali da ake samu a tsarin sauti. Ra’in Ishara Wannan ra’i ya yi da’awar cewa, harshe ya samu ne daga isharori. Babbar hujjar da wannan ra’i ya dogara da ita, ita ce masu amfani da harsuna daban-daban na amfani da isharori a-kai-a-kai a cikin maganganunsu. Misali, mabaraci mai jin yunwa na yin ishara ta hanyar taba bakinsa da shafa cikinsa domin nuna halin da yake ciki na yunwa. Ta irin wannan hanya ce wannan ra’i yake ganin mutanen farko suke sadarwa a tsakaninsu. Raunin Ra’i a. Wannan ra’i ya kasa nuna yadda ishara ta zama harshe Daga qarshe, duk da raunin wannan ra’i, masana na ganin wannan ra’i ya fi ragowar ra’a’yoyi kama da gaskiya dangane da asalin harshe.