Abdulmumini Kabir Usman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdulmumini Kabir Usman
Rayuwa
Haihuwa 1951 (72/73 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci

Sarki Abdulmumini Kabir Usman (An haife shine a shekara ta alif dari tara da hamsin da daya (1951). Shine sarkin Katsina mai ci, da ne kuma ga tsohon Sarki Muhammad Kabir, jika ne kuma ga Sarki Usman Nagogo da Muhammad Dikko.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Alhaji Abdulmumini Kabir Usman shi ne sarki na arba’in a jerin sarakunan Katsina, sannan kuma sarki na goma (10) a jerin sarakunan Fulani, kuma sarki na huɗu a zuriyar Sulluɓawa.[1] {{Ana bukatan hujja}

Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, mutum ne mai matuƙar son karatu, a saboda haka ya kasance mai ilimin addini da na zamani kamar mahaifinsa. Haka nan kuma shi mutum ne mai son jama’arsa, wannan abu ne mai sauƙin tantancewa, da isar ka fadar Katsina ka ga yadda mutane ke kaiwa-da-komawa ba tare da wata fargaba ko ɗari-ɗari ba.

Jagora ne shi kuma abin koyi, mutum ne mai fasaha, jarumtaka da kuma gogewa a harkar mulki. Shi ne sarkin Katsina na farko wanda ke da digiri a kansa.[2]

Haihuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Am haifi Alhaji Abdulmumini Kabir Usman a ranar tara 9 ga watan Janairun shekarar alif dari tara da hamsin da daya 1951. Shi ɗa ne ga sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman, wanda shi kuma ɗa ne ga sarkin Katsina Usman Nagogo, shi kuma ɗa ga sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman, ya yi karatunsa na firamare a makarantar firamaren kwana (Dutsinma Boarding Primary School) ta Dutsinma, daga shekara ta alif 1959 zuwa shekara ta alif 1964. Daga nan kuma ya cigaba zuwa makarantar sakandiren gwamnatin Katsina (Government Secondary School, Katsina) wacce daga baya ta koma kwalejin gwamnati ta Katsina (Government College Katsina), daga shekara ta alif 1965 zuwa shekara ta alif 1969. Bayan kammala wannan makaranta ya samu zarcewa zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga shekara ta alif 1972 zuwa shekara ta 1974. A ƙarshe ya samu nasarar samun digiri a fannin soshiyoloji (Bachelor's Degree in Sociology) daga Jami’ar Ɗanfodiyo da ke jihar Sakkwato.

Gogayyar Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya zama Magajin Garin Katsina Hakimin Birni da kewaye lokacin yana ɗan shekara 30 a duniya. Yana kan wannan muƙami na Hakimin Birni da kewaye wanda a lokacin Katsina tana matsayin ƙaramar hukuma a Jahar Kaduna, sai aka ɗaukaka darajar Katsina zuwa jaha a shekarar 1987.

Ya riƙe muƙamai da dama, daga ciki akwai zamowarsa shugaban Jami’ar Oba-Femi Awolowo tun daga shekarar 2008 har zuwa shekarar 2015 inda aka canja shi zuwa shugabancin Jami’ar Ilorin.

Ya yi aiki a matsayin chairman na wasu ƙungiyoyi da ma’aikatun gwamnati da hukumomi da aka yarda cewa sun haura 71.

Zamowarsa Sarki[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2008 aka ayyana sunan Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman a matsayin sarkin Katsina, bayan da masu zaɓen sarki suka zaɓe shi a matsayin sabon sarkin Katsina bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Muhammadu Kabir Usman. An yi bikin naɗinsa aranar 5 ga watan Yuli na shekarar 2008.

Gudunmawa[gyara sashe | gyara masomin]

Mutum mai son jama’a da kuma yi musu hidima kamar Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman, abu ne mai wuya a iyakance irin gudunmawar da yake baiwa jama’a. Alƙaluma sun kasa ƙididdige ɗimbin mutanen daya ya samawa guraben karatu a jami’o’in ciki da wajen Nijeriya.

Sakamakon irin ayyukan taimakon al’umma da yake yi, ya samu kyaututtuka na girmamawa, kamawa tun daga ƙaramar hukumar Katsina, har zuwa matakin jaha har zuwa matakin tarayya inda aka bashi lambar yabo mai taken “Commander of the Federal Republic (CFR)”.[3] [4] [5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Buhari, Dimeji in Katsina for Emir's Coronation". AllAfrica. 6 July 2008. Retrieved 7 June 2010.
  2. "Yar'Adua accuses lecturers of corruption". The Punch. 21 December 2008. Archived from the original on 13 April 2009. Retrieved 7 June 2010.
  3. https://www.myheritage.com/names/kabir_usman%20nagogo
  4. https://allafrica.com/stories/200803140804.html
  5. https://peoplepill.com/people/abdulmumini-kabir-usman/