Umar Farouk Abdulmudallab

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Umar Farouk Abdulmutallab An haife shi a Disamba 22, 1998, anfi sanin sa da Underwear Bomber, dan asalin Najeriya ne lokacin da yana dan shekara 23 aka same shi da laifin boye abu mai fashewa a rigar sa tare da kokarin tayar da shi a wani jirgi mallakin kasar Amurika wato Northwest Airlines Flight 263, akan hanyar sa daga Amstadam zuwa Detroit, jihar Michigan, ranar Kirsimati ta 2009.

Simpleicons Interface user-outline.svg Umar Farouk Abdulmudallab
UmarFarouk.jpg
Rayuwa
Haihuwa Lagos, 22 Disamba 1986 (32 shekaru)
ƙasa Nijeriya
Yan'uwa
Mahaifi Umaru Mutallab
Karatu
Makaranta University College London Translate
Sana'a
Sana'a engineer Translate da terrorist Translate
Imani
Addini Musulunci

Tarihin sa[gyara sashe | Gyara masomin]

Umar Farouk Abdulmutallab shine auta daga yayan mahaifinsa su 16. Mahaifin sa shine Alhaji Umaru Mutallab, mai arziki kuma babban dan kasuwa, ma'aikacin banki, tsohon shugaban bankin First Bank, tsohon kwamishina a ma'aikatar cigaban tattalin arziki a Najeriya. Jaridar The Times ta ayyana Alhaji Abdulmutallab a matsayin daya daga cikin shahararun attajirai a Afrika. Ma haifiyar Umar Aisha, itace ta biyu daga cikin matan mahaifin sa. Asalin iyalan sun taso ne daga gatin Funtua na jihar Katsina. Amma shi Abdulmutallab ya taso ne a Garmin Kaduna dake Arewacin Najeriya a lokacin yarintar sa yayi karatu a makarantar Essence International School Ya kuma yi karatu a makarantar Rabiatu Mutallib Institute for Arabic and Islamic Studies, ya kuma yi karatu a makarantar The British School dake a birnin Lome, Togo. An baiyana shi da cewar shi zakakurin dalibi ne kuma yana sha'awar wasan kwamfuta na Play Station da wadan kwallon kwando.

Abdulmutallab ya kammaka karatu a University College dake birnin Landan a watan Satumba na 2005 inda ya samu digiri a fannin Injiniyanci da harkar Kudi da Kasuywanci. Ya kuna samu digirin injiniyancin kanikanci a watan Yuni na 2008.

A tabakin kawunnan sa, a lokacin da yana kankanin yaro yana da kishin addinin Musulunci, According to one of his cousins, as a teenager. Ya kuma sha Yin watsi da harkokin bankin da Mahaifin sa yake yi inda yake kallon hakan a matsayin haramtaccen kasuwanci tare da kuma nuna ma mahaifin sa da ya dakatar da duk wata hilda da aikin banki.

Kokarin sa na yin kuna bakin wake[gyara sashe | Gyara masomin]