Jump to content

Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Katsina

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Katsina

Excellent in Education
Bayanai
Suna a hukumance
Federal College of Education, Katsina
Iri school of education (en) Fassara da jami'a
Ƙasa Najeriya
Harshen amfani Turanci
Tarihi
Ƙirƙira 1976
fcekatsina.edu.ng
hoton daliban colejin ilimi ta katsina
college
federal college
federal college of education
college

Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Katsina cibiyar ilimi ce ta gwamnatin tarayya da ke Katsina, Jihar Katsina, Najeriya.

Tana da alaƙa da Jami'ar Bayero Kano don karatun digiri. Shugaban makarantar na yanzu shine Aliyu Idris Funtua.[1]

An kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical) Katsina a shekarar 1976.[2]

Laburaren Kwaleji, ɗakin karatu ne wanda aka kafa a shekara ta 1975 a matsayin babban ɗakin karatu na kwalejin. Laburare na da litattafai sama da dubu 50,000, gami da wurin zama da zai iya ɗaukar mutane 500 alokaci guda, tare da kayan lantarki - ɗakin karatun na da kwamfutoci sama da 100 gami da sabis na shiga yanar gizo ko intanet.[3] Akwai isassun kayan aiki a dakin karatun don samun sauƙin bayanai game da dalibai, kuma suka dace da darussan da ake koyawa a kwalejin. Babban ɗakin karatu ne ke kula da sauran ɗakunan karatu na sashe a cikin makarantar.[3]

Cibiyar tana ba da darussa kamar haka;[4]

  • Ilimin Kimiyyar Noma
  • Ilimi da Lissafi
  • Fine And Applied Arts
  • Ilimin Kimiyya
  • Ilimin Gina Fasaha
  • Ilimi da Ingilishi
  • Ilimin Kwamfuta
  • Ilimi da Hausa
  • Ilimi da Larabci
  • Ilimin Fasaha
  • Ilimin Halitta
  • Ilimi da Ilimin zamantakewa
  • Tattalin Arzikin Gida da Ilimi
  • Hadaddiyar Kimiyya
  • Ilimin Kasuwanci
  • Karatun Ilimin Firamare

Alaƙa da Tsari

[gyara sashe | gyara masomin]

Cibiyar tana da alaƙa da Jami'ar Bayero Kano don bayar da shirye-shiryen da za su kai ga samun digiri na farko (B.Ed.) a;

  • Ilimi da Physics
  • Ilimi da Chemistry
  • Ilimi da Ingilishi
  • Ilimin Jiki da Lafiya
  • Ilimi da Ilimin Addinin Musulunci
  • Ilimi da Larabci
  • Ilimi da Biology
  • Ilimi da Lissafi
  • Ilimi da Hausa

Makarantar baya ga shaidar kwalin NCE da take badawa kuma ana degree (undergraduted) a makarantar. Kuma cibiyar tana dora ɗalibai zuwa wuraren aiki don samun ƙwarewar aiki ta hanyar shirin SIWES.

  1. "Just In: President Buhari reappoints Dr. Aliyu Idris Funtua as Provost FCE Katsina". Katsina Post (in Turanci). 2020-07-10. Archived from the original on 2021-08-13. Retrieved 2021-08-13.
  2. "HISTORY – FEDERAL COLLEGE OF EDUCATION KATSINA" (in Turanci). Retrieved 2021-08-13.
  3. 3.0 3.1 "Federal College of Education, Katsina". fcekatsina.edu.ng. Retrieved 2022-12-05.
  4. "List of Courses Offered at Federal College Of Education Katsina (FCEKATSINA)". Nigerian Scholars (in Turanci). 2018-03-06. Retrieved 2021-08-13.

Hanyoyin hadin waje

[gyara sashe | gyara masomin]