Aliyu Idris Funtua
Aliyu Idris Funtua | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Funtua |
Sana'a |
Dakta Aliyu Idris Funtua shehin malamin boko ne kuma shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Katsina, Jihar Katsina. Ya zama shugaba na 13 da ya riƙe wannan muƙamin a kwalejin, biyo bayan samun amincewar Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 19 ga watan agustan shekarar, 2016[1][2][3] Ko kafin wannan nadi, shi ne mataimakin shugaban Kwalejin kuma mai rikon kwarya. A shekarar, 2020 ne aka sake sabunta muƙaminsa na Shugaban Kwalejin Ilimi ta Katsina. Shi dai Dakta Aliyu Idris Funtua na da digirin digirgir daga Jami'ar Bayero ta Kano wanda ya samu a shekara ta, 2016.[4].[Ana bukatan hujja]
Farkon rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Dakta ya fito ne daga Karamar Hukumar Funtua da ke Jihar Katsina. Mai Marbata Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman ya ba Dakta Aliyu Idris Funtua sarautar 'Wakilin Malaman Katsina' a shekarar, 2018. Wannan na daga cikin sarautun da yake da su.[5]
Asali
[gyara sashe | gyara masomin]Shi dai Dakta an haifeshi ne a garin Dandume a shekarar, 1962 amma ya taso ne a garin Funtua inda yayi firamare ta Aya watau (Aya Primary School) a garin na Funtua sai yayi makarantar gaba da piramare a garin Malumfashi. Ya samu shedar Malanta daga Kwalejin Ilmi ta Katsina a shekarar, 1984. A Jami'ar Bayero ta Kano ne ya yi karatun digirinsa na farko da na biyu da na uku a Kimiyyar Harshen Hausa.[6]
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan koyarwa da yayi a Makarantar Sakandare ta Gwamnati dake Gwoza a tsakanin shekarar, 1984 zuwa 1985, Malam Aliyu idris Funtua ya fara aiki da Jihar Kaduna ta da a matsayin malamin kuma ya riƙe mukamai daban-daban har zuwa shekarar, 1997 lokacin da ya zama mataimakin shugaban makarantar sakandare.
Likkafa ta ci gaba a lokacin da Dakta Funtua ya zama malamin kwaleji a shekara ta, 1997 kuma ci gaba da bada gudunmuwarsa a fagen da ya kware da kuma riƙe mukamai daban-daban.[5] Bayan samar da Jami'ar Umaru Musa Yar'adua Katsina, an ɗauki aron Dakta inda ya koyar tun daga shekarar, 2009 zuwa 2010. A shekarar, 2011 ne Dakta ya kai matakin Babban Laccara watau (Chief Lecturer).[5]
Iyali
[gyara sashe | gyara masomin]Dakta Aliyu Idris Funtua na da iyali da yara.[7][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://dailytrust.com/fce-obudu-provost-assumes-work/
- ↑ Webmaster (2016-08-26). "FCE Katsina gets new provost". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-02-20.
- ↑ "FCE Katsina, Obudu get new provosts | The Nation Newspaper". The Nation Newspaper. (in Turanci). 2016-08-26. Retrieved 2023-02-20.
- ↑ Webmaster (2016-09-01). "FCE Obudu provost assumes work". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2023-03-04.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 Mustapha, Olusegun (2018-04-13). "Dokta Aliyu Funtuwa ya zama wakilin Malaman Katsina". Aminiya (in Turanci). Retrieved 2023-02-20.
- ↑ https://thesourcereporters.wordpress.com/2022/11/05/dr-aliyu-idris-six-years-on-the-saddle/
- ↑ "Buhari Appoints Two New Provosts for FCEs Obudu, Katsina – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2023-02-24.
- ↑ https://www.thisdaylive.com/index.php/2016/08/26/buhari-appoints-two-new-provosts-for-fces-obudu-katsina/