Hasumiyar Gobarau
Hasumiyar Gobarau | |
---|---|
| |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jiha | Jihar Katsina |
Birni | Katsina |
Coordinates | 12°59′53″N 7°35′44″E / 12.997977°N 7.595517°E |
![]() | |
Heritage | |
|
Hasumiyar Gobarau na daya daga cikin dogayen gine-ginen tarihi a Jihar Katsina, dake Arewacin Nijeriya kuma an yi hasashen cewa an gina ta wajen shekaru sama da 600 da suka gabata. An gina hasumiyar da irin tsarin gine-ginen Mali. Tarihi ya tabbatar da cewa an gina ta ne domin bautar Allah wato Masallaci kenan, kuma daga bisani hasumiyyar ta dauki gurbin tsare garin daga mahara, ta hanyar hango abokan gaba kafin su iso cikin birnin Katsina. A yau hasumiyar na ɗaya daga cikin alamun ita kanta Katsina, wadda kan jawo mutane daban daban masu yawon bude ido su zo birnin Katsina.
Hasumiyar ita ce masallacin Juma’a na farko a tsohon birnin Katsina, wanda aka gina tsakanin shekarar 1348 zuwa 1398, sannan akwai kasuwa kusa da gefenta. Asalinta ta fi yadda take a yau tsawo. Wasu masana sun ce ta ninka yadda take a yanzu. Bugu da kari hasumiyar ta fadi, domin rashin kulawa, musaman a zamanin mulkin Sarkin Katsina Umarun Dallaje; domin a lokacin an fi mayar da hankali kan yada jihadi tare da koyarwa da tabbatar da adalci tsakanin mutane. Sai a zamanin Sarki Dikko aka kara gina ta, bayan ta zagwanye tare da yi wa hasumiyar kwaskwarima.
Bugu da kari, daga bisani da aka gina masallacin Juma’a watau masallacin dutse a kusa da kofar Soro, a karni na sha takwas sai aka karkata can, a yayin da malamai suka rika Salla a masallatan unguwanni ko a zaurukan da suke koyarwa. Haka ya kara rage yawan masu zuwa Gobarau.[1]
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ "Gobarau, Story of the 664 year old Minaret". Daily Trust Newspapers. Archived from the original on 2 September 2019. Retrieved 2 September 2019.