Kaaba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Kaaba
cubic building, holy place
ƙasaSaudi Arebiya Gyara
located in the administrative territorial entityMakkah, Hijaz Gyara
coordinate location21°25′21″N 39°49′34″E Gyara
significant eventƊawafi Gyara
IPA transcriptionˈkaʕ.ba Gyara
Unicode character🕋 Gyara

Kaaba (Larabci ٱلْـكَـعْـبَـة‎ Ka'abah) ana kuma kiran ta da al-Kaʿbah al-Musharrafah (Larabci ٱلْـكَـعْـبَـة الْـمُـشَـرًّفَـة‎ Daki mai tsarki), wani ginannen daki ne a birnin Makka na kasar Saudiyya mai matukar tsarki a tsakani Misulmai. (ٱلْـمَـسْـجِـد الْـحَـرَام‎ Al-Masjid Al-Ḥarām, Masallacin Harami), Har ila yau kuma Musulmai kan kira shi da (بَـيْـت ٱلله‎ Dakin Allah). Duk inda suke a duniya Musulmai ana bukatar su da su fuskanci bangaren wannan dakin lokacin gabatar da Sallah (صَـلَاة‎ Ṣalât, Bautar Allah a Musulunce). Dakin kuma shine ake kira da (قِـبْـلَـة‎ qiblah, mafuskanta) wato dai mafuskantar ta musulmai domin gabatar da Sallah.

Daya daga cikin shika shikan Musulunci biyar shine aikin Hajji حَـجّ‎, a dakin na Kaaba ne matattarar mahajjatan, kuma kowanne Musulmi yana da fatan zuwa dakin koda sau daya ne a rayuwar sa domin dawafi (طَـوَاف‎ tawaf, kewaya dakin sau bakwai da niyyar bauta ma Allah). Hakanan ma bayan aikin Hajji haka dai musulman na yin dawafin a fakin yayin zuwansu Umara (عُـمْـرَة‎ Umrah). Miliyoyin mutane ne ke ziyartar dakin domin tsarkake Allah, mutane daga wajen kasar Saudiyya 1,379,531 ne suka halarci dakin yayin aikin hajji na 2013, a shekarar 2014 ma Saudiyya ta sanar da adadin mahajjata daga wajen kasar ta 1,389,053 wadan da suka halarci hajjin shekarar yayin da yan kasar ta kuma kimanin mutane 63,375 ne suka samu halar ta.

Tsarin gini[gyara sashe | Gyara masomin]

Zanen kaaba da rabe raben ta
Zanen kaaba wanda yake nuni da wuraren ta.