Kubra Dako

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kubra Dako

Tsohuwar jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud, tayi zamani da dadewa tayi fina finai da dama a masana'antar kafin ta bar masana'antar. Tayi tashe tare dasu fati muhammad , maryam hiyana, abida muhammad,Maryam Umar,hadiza kabara, zuwaira Juda da sauran su. Kyakkyawar mace acikin yammatan kanniwud bakar fata ce kyakkyawa Mai manyan idanuwa, ita tayi fim din fati yar Adamawa Wanda sukai da nura Hussain.[1]

Takaitaccen Tarihin Ta[gyara sashe | gyara masomin]

cikakken sunan ta shine Kubra Alhaji Abdullahi dacko ,Wanda mutane suka Santa da kubra dako, An haife ta a watan June takwas ga watan a shekara ta alif dari tara da tamanin da hudu 1984, Haifaffiyar jihar niger ce mahaifin ta babban mutum ne a jihar.[2]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Kubra tayi karatun firamare da sakandiri a garin naija, daga Nan ta taho jami'ar Bayero university Kano inda ta Karanci sociology. Tana karatu ta hadu da jarumi Margayi Ahmad S Nuhu Wanda shine ya SATA a masana'antar fim ta fara da fim Mai suna"gata"daga Nan tayi fina finai sunfi Dari inda ta shahara a masana'antar. Ta dauki shekaru shida a masana'antar daga shekara ta dubu biyu da hudu 2004 zuwa 2010, daga nan aka daina ganin ta a fim.

Fina finan ta.

  • Gata
  • Tutar so
  • Fati yar Adamawa
  • Taron dangi
  • Hausa bakwai
  • Dare da yawa
  • [3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.hausaloaded.com/2019/08/kalli-hotun-jaruma-kubrah-dako-da-ya.html
  2. https://hausa.legit.ng/1254584-bayan-shafe-shekaru-ba-a-ji-duriyarta-ba-jaruma-kubura-dako-ta-bayyana-cikin-wani-yanayi-a-wani-hoto.html
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-29. Retrieved 2023-07-29.