Kura Tandu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kura Yanzu maɗauki ne wanda ake yinsa domin ajiyar mai musamman man gyaɗa da soyayyen man shanu. Ana yin waɗannan maɗaukan ne musamman da fatar dabbobi wadda aka jeme. Sannan kuma ana yin ta musamman da ƙarfe. Salon tsara ta ya ta'allaƙa ne a kan irin abinda ake so ayi da ita, misali idan Kura Tandun doguwar ajiya ne to ana yin sa da bambanci da wanda ake yin shi domin zuba mai na amfanin gida na yau da kullum.

Kura Tandu ya kasu kashi biyu, bayan wanda ake ajiyar mai kuma akwai maɗaukin kwalli. Shine wanda ake yinsa domin zuba niƙaƙƙen kwalli.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://bahaushiyaonline.wordpress.com/author/bahaushiyaonline/page/2/